Ƴan majalisar Adamawa 15 da kakakin majalisa sun fice daga PDP gabanin sauyin sheƙar Fintiri
Wasu ƴan majalisar dokokin jihar Adamawa guda 15 sun yi murabus daga jam’iyyar PDP.
Kakakin majalisar, Bathiya Wesley, ne ya sanar da ficewar ‘yan majalisar a zaman majalisa na ranar Laraba.
Wesley ya ce shi ma tare da mataimakinsa, Buba Jijiwa, sun fice daga jam’iyyar mai mulki a jihar.
Ƴan majalisar sun danganta ficewar tasu da “rikicin da ya daɗe yana ci gaba” a cikin PDP.
“Dukkan wasiƙun da aka karanta suna ɗauke da saƙo iri ɗaya. Mambobin PDP sun nuna rikicin da ke faruwa a matakin ƙasa na jam’iyyar a matsayin babban dalilin da ya sa suka yanke shawarar ficewa,” in ji Wesley.
“Sun kuma yaba wa PDP bisa ba su damar tsayawa takara da kuma cin zaɓe a ƙarƙashin tutar jam’iyyar.”
Daga cikin ‘yan majalisar da suka fice akwai Kefas Calvin, Bulus Geoffrey, Haruna Jilantikiri, Kefas Emmanuel, Ahmed Belel, Moses Zah, Kate Mamuno, Pwamwakeno Mackondo, Adun Alaba, Bulus Kantom, Musa Kallamu, da Japhet Hammanjabu.
Jaridar TheCable ta rawaito cewa ‘yan majalisar sun koma jam’iyyar APC, sai dai har yanzu ba su bayyana hakan a hukumance ba.
Ana kuma cewa gwamnan jihar, Ahmadu Fintiri, na kammala shirye-shiryen komawa jam’iyyar mai mulki.
A ranar Asabar, Fintiri ya karɓi jagororin APC na jihar a liyafar buɗa-baki a gidan gwamnati da ke Yola, babban birnin jihar Adamawa.
Comments
Post a Comment