Iran ta kai harin ramuwar gayya kan Israel da Amurka
An ji karar fashe-fashe a yankin Haifa da ke arewacin Isra’ila a ranar Asabar bayan harba makamai daga Iran, kamar yadda kafar yada labarai ta Isra’ila Ynet ta rawaito. Tun da fari, kararrawar gargadin hare-haren sama ta yi kara a sassa daban-daban na Isra’ila bayan da sojojin kasar suka sanar da gano makamai masu linzami da aka harba daga Iran zuwa cikin kasar. A safiyar Asabar ne Isra’ila ta kaddamar da wani hari kan Iran mai taken “Lion’s Roar”, inda ta ayyana dokar ta-ɓaci ta musamman da gaggawa a fadin kasar. A nasa bangaren, Shugaban Amurka, Donald Trump, ya tabbatar da cewa ana gudanar da “manyan ayyukan yaki” a Iran, yana mai cewa manufar hakan ita ce kare al’ummar Amurka ta hanyar “kawar da barazanar da ke tafe daga gwamnatin Iran.” Gidan talabijin na kasar Iran ya kuma rawaito cewa sojojin Iran na kai hare-hare kan sansanonin sojojin Amurka da ke yankin.