Posts

Showing posts from March, 2026

Alleged 419 Case: Senator Abdu Kwari in Fresh Court Battle Over Property Deal

Image
Proceedings continued today, March 30, 2026, at the High Court of Justice, Dogarawa in Zaria, Kaduna State, presided over by Justice Yakubu Badamasi, in the ongoing criminal trial involving Abdu Kwari, Hajiya Amina Dalhatu Akilu, and Shehu Abdu Kwari over allegations of fraud and criminal conspiracy. The case arose from a petition filed by a Zaria-based businessman, Ahmed Muhammad Gusau, who accused the defendants of fraudulently inducing him into a property exchange deal. According to the complainant, he surrendered his residential property located at No. 17 Sale Annur Street, Kabama Layout, Sabon Gari, Zaria, valued at ₦60 million, in exchange for a plot of land at No. 5 Abubakar Mustapha Road, Kabama Layout, allegedly owned by Senator Abdu Kwari and valued at ₦20 million. He further alleged that he was informed the Senator does not sell land but only engages in property exchange arrangements. Based on this understanding, he accepted the offer and proceeded with the trans...

Bola’ige Backs Youth Development as Gyallesu United Win Zaria Tournament

Image
The final match of the Solidarity Coaches Zaria Gala Jamboree ended in excitement and celebration as Gyallesu United defeated Santos F.C 2–1 to lift the prestigious trophy. Gyallesu United were officially crowned champions of the tournament, while Santos F.C finished as runners-up after a hard-fought performance. The tournament, which featured participation from 12 teams, was fully sponsored by Mahmud Lawal Isma’ila Bola'ige, a member of the Kaduna State House of Assembly representing Zaria City Constituency. In his address at the event, Bola’ige expressed his commitment to youth development through sports, emphasizing the importance of grassroots football in promoting unity and talent discovery. He commended the Governor of Kaduna State, Uba Sani, for his continuous support and investment in sports development across the state. He also praised the Speaker of the House of Representatives, Abbas Tajudeen, for his leadership and contributions to youth empowerment initiati...

Hadimin Shugaban Nijeriya, Ja’oji ya ajiye mukaminsa domin tsayawa takara a zaɓen 2027

Image
Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Nijeriya kan harkokin zama ɗan ƙasa da shugabanci, Nasir Bala Aminu, ya ajiye aikinsa gabanin zaɓen 2027. Matakin na zuwa ne bayan umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu cewa duk masu riƙe da muƙaman siyasa da ke son tsayawa takara su sauka kafin ƙarshen Maris 2026. Ja’oji ya gode wa shugaban ƙasa bisa damar da aka ba shi, yana mai cewa an naɗa shi ne domin ƙarfafa matasa su taka rawa wajen gina ƙasa. Rahotanni sun nuna cewa yana shirin tsayawa takarar kujerar majalisar wakilai ta Tarauni, yayin da magoya bayansa ke nuna goyon baya ga burinsa na siyasa.

Ƴansanda sun kama wata mata da ake zargi da satar kayayyaki na N10.1m a Katsina

Image
Rundunar ‘yansanda a jihar Katsina ta kama wata mata mai shekaru 27, Hadiza Ibrahim, bisa zargin satar kayayyaki daga wani shago da darajarsu ta kai naira miliyan 10.1. Mai magana da yawun rundunar, DSP Aliyu Abubakar, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, inda ya ce an kama matar ne bayan samun rahoto daga jami’in tsaron shagon Green House da ke Katsina a ranar 4 ga watan Maris. A cewarsa, an bayyana matar a matsayin gogaggiyar ‘yar satar shago da ke gudanar da ayyukanta a cikin birnin. Abubakar ya ce kayayyakin da aka sace sun kai kimanin naira 10,102,000, yana mai cewa an gano laifin ne ta hanyar hotunan CCTV na shagon, inda aka hango matar tana satar kayayyaki daban-daban. “Bayan nazarin bidiyon CCTV, an bi sahunta har zuwa inda aka kama ta,” in ji shi. Ya kara da cewa bayan gudanar da bincike a gidanta, an gano kayayyaki masu darajar wannan kudi. Kayayyakin da aka kwato sun hada da takalma guda 274, mayafi guda 37, kayan wasanni guda 67, ka...

Mahaifiyar tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ta rasu

Image
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya yi rashin mahaifiyarsa, Hajiya Umma, wadda ta rasu a ranar Juma’a. An tabbatar da rasuwar ne cikin wata sanarwa da iyalan El-Rufai suka fitar a ranar Juma’a, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito. Majiyoyi sun bayyana cewa marigayiyar ta dade tana fama da matsalolin lafiya da suka shafi tsufa, waɗanda suka ƙara tsananta a ‘yan kwanakin nan. A cewar majiyoyin, yanayin lafiyarta ya ƙara tabarbarewa bayan ta samu labarin tsare ɗanta da hukumar ICPC ta yi.

Zarge-zarge Na Bin Yuguda Yayin da APC Ta Ba Shi Mukami

Image
By Ibrahim Shehu, Abuja  A daidai lokacin da Jam’iyyar APC ke kokarin tabbatar ƙarfafa ladabi a cikin gida, sahihanci da kuma amincewar jama’a, nada tsohon gwamnan Jihar Bauchi, Isa Yuguda, a matsayin Sakatare na kwamitin shirya babban taron jam’iyyar ya jawo muhawara mai zafi a tsakanin masu lura da al’amuran siyasa da kuma membobin jam'iyyar a matakin jiha da tarayya. A karkashin jagorancin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, APC ta kasance a matsayin jam’iyya mai kishin gyara, gaskiya da kuma ingantaccen shugabanci. Sai dai wannan mataki na baya-bayan nan ya haifar da tambaya mai muhimmanci: shin jam’iyyar da ke son samun amincewar jama’a za ta iya bai wa mutum da ake yawan danganta shi da zarge-zargen cin hanci irin wannan muhimmiyar rawa? Rahotanni da dama daga baya sun danganta mulkin Isa Yuguda (2007–2015) da wasu manyan zarge-zarge. Daga ciki akwai zargin badakalar kwangiloli da kudaden da ba a iya tantance su ba, wanda aka kiyasta ya haura Naira biliyan 212.2. Hak...

Between Reform and Reality: Yuguda’s Appointment Sparks Debate

Image
By Ibrahim Shehu, Abuja At a time when the All Progressives Congress (APC) is striving to reinforce internal discipline, credibility, and public trust, the appointment of former Bauchi State governor, Isa Yuguda, as Secretary of the party’s Convention Committee has sparked intense debate among political observers. Under the leadership of President Bola Ahmed Tinubu, the APC has consistently projected itself as a party committed to reform, accountability, and progressive governance. However, this recent decision raises a fundamental question: can a party that seeks to inspire confidence afford to place individuals burdened by persistent allegations of corruption. Public records and multiple reports over the years have linked Isa Yuguda’s tenure as governor (2007–2015) to a range of serious allegations. Among them are claims of contract fraud involving unaccounted sums estimated at over ₦212.2 billion. There have also been allegations bordering on abuse of office, diversion o...

Ayyukan tituna a Kaduna za su taimaka wajen samun nasarar Uba Sani a 2027 - KADRA

Image
Manajan darakta na hukumar kula da tituna ta Jihar Kaduna (KADRA), Dakta Abdullahi Baba-Ahmed, ya ce manyan ayyukan tituna da ake yi a fadin jihar za su ƙara wa Gwamna Uba Sani ƙarfi wajen samun nasara a zaɓen 2027. Ya bayyana haka ne yayin da yake karɓar wata ƙungiyar matasa, inda ya ce gwamnatin Sani ta aiwatar da sama da ayyukan tituna 140, masu tsawon kusan kilomita 1,335 cikin shekaru uku, wanda ya ce ba a taɓa irin sa ba a Arewa. A cewarsa, fiye da kashi 60 cikin 100 na ayyukan sun kammala, yayin da ake sa ran kammala sauran kafin ƙarshen wa’adin farko na gwamnati. Baba-Ahmed ya ce ayyukan sun shafi dukkan yankunan jihar, har da karkara da wasu al’umma ke ganin irin waɗannan ayyuka a karon farko cikin shekaru da dama. Ya ƙara da cewa titunan sun taimaka wajen sauƙaƙa zirga-zirga, bunƙasa kasuwanci da kuma haɗa al’umma. Daga cikin manyan ayyukan akwai titin Gadar Gayan–Kujama mai tsawon kilomita 35 da gada a kan kogin Kaduna, wanda ya ratsa ƙauyuka 76. Ya b...

Ministan wutar lantarki ya nemi afuwar ’yan Najeriya kan matsalar wuta

Image
Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya nemi afuwar ’yan Najeriya kan yawan katsewar wutar lantarki da ake fuskanta a ƙasar nan. Ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja, inda ya amince cewa matsalar ta jawo wahala ga gidaje, kasuwanci da masana’antu, musamman a lokacin zafi. Adelabu ya ce ana sa ran samun sauƙi cikin makonni biyu masu zuwa, sakamakon gyaran bututun gas da kuma alkawuran masu samar da iskar gas. Ya kuma ce gwamnati ta kafa kwamiti domin sa ido kan yadda kamfanonin gas ke cika alƙawuran samar da iskar da ake buƙata domin samar da wutar lantarki. Ministan ya jaddada cewa gwamnati na aiki tukuru domin inganta samar da wuta tare da cimma burin samar da megawatt 6,000 kafin ƙarshen shekarar 2026. Ya ƙara da cewa matsalar na da alaƙa da ƙarancin gas, tsofaffin kayayyakin aiki da kuma wasu matsalolin tsarin wutar lantarki a ƙasar.

Bauchi APC: When Politics Turns to Accusations Without Proof

Image
Bauchi APC: When Politics Turns to Accusations Without Proof By Usman Dahiru, Bauchi  The unfolding political drama within the All Progressives Congress (APC) in Bauchi State has taken a troubling turn, with former governor Isa Yuguda resorting to sweeping allegations against the Minister of Foreign Affairs, Yusuf Tuggar. However, beyond the noise, a more critical question emerges: are these claims rooted in verifiable facts, or are they part of a calculated political strategy to weaken a perceived rival? A careful examination of the accusations reveals a pattern that is all too familiar in Nigeria’s political landscape serious claims made without publicly available evidence. Allegations of bribery, internal sabotage, and deliberate destabilisation of the party are weighty issues that demand proof, not press statements. In the absence of such evidence, they risk being viewed as politically motivated narratives aimed at discrediting Tuggar’s rising profile within the APC...

Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Tambuwal/Kebbe a jihar Sokoto, Abdussamad Dasuki ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP, inda ya koma ADC

Image
Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Tambuwal/Kebbe a jihar Sokoto, Abdussamad Dasuki ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP, inda ya koma ADC. A cikin wasiƙar da ya aika wa shugaban PDP na mazabar Dogon Daji/Salah Ward a ƙaramar hukumar Tambuwal, mai ɗauke da kwanan wata 15 ga Maris, 2026, Dasuki ya ce rikicin shugabanci da ya daɗe yana addabar jam’iyyar ne ya sa ya yanke shawarar barin jam’iyyar. Ya bayyana cewa matsalolin cikin gida na jam’iyyar sun raunana ƙarfin PDP wajen taka rawar da ta kamata a matsayin babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya. Dan majalisar ya ce ya ɗauki matakin ne bayan tattaunawa da abokan siyasarsa da kuma al’ummar mazabarsa, inda suka nuna damuwa kan halin da jam’iyyar da kuma ƙasar ke ciki.

Gwamna Abba ya rushe ma’aikatar ilimi mai zurfi yayin da mataimakin Gwamna ya rasa mukamin sa na kwamishina

Image
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da rushe Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi ta jihar, matakin da ya sa Mataimakin Gwamnan jihar, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya daina rike mukamin kwamishinan da ke kula da ma’aikatar. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Lahadi. Sanarwar ta ce gwamnatin jihar ta hade Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi da Ma’aikatar Ilimi domin karfafa daidaiton gudanarwa tare da hanzarta aiwatar da gyare-gyare a bangaren ilimi a jihar. A karkashin sabon tsarin, ma’aikatar da aka hade za ta ci gaba da aiki ne a karkashin suna Ma’aikatar Ilimi. Haka kuma za a kafa wani sashe na musamman mai kula da Ilimi Mai Zurfi a cikin ma’aikatar domin kula da harkokin manyan makarantu. Sanarwar ta kara da cewa wannan sashe zai kasance karkashin jagorancin Babban Sakatare tare da samun goyon bayan ma’aikatan da suka dace domin tabbatar da ingantaccen gudanar da cibiyoyin ilimi mai zurfi a jihar. Har ila yau, duk...

Sanata Wamakko ya rabawa marayu 10,000 tallafin Naira dubu daya, daya kowannen su a Sokoto

Image
Sanata Wamakko ya rabawa marayu 10,000 tallafin Naira dubu daya, daya kowannen su a Sokoto Tsohon gwamnan Jihar Sokoto, Sanata Aliyu Wamakko, ya bayar da tallafin naira miliyan 10 da kuma kala 100 na kayan sawa domin tallafa wa marayu da sauran marasa galihu gabanin bikin Sallah. An miƙa tallafin ne ta hannun hukumar zakka da Waqafi ta Jihar Sokoto (SOZEA), inda shugaban hukumar, Lawal Maidoki, ya karɓa a ranar Asabar a Sokoto. Sanata Wamakko, mai wakiltar Sokoto ta Arewa a majalisar dattawa, ya ce tallafin na da nufin taimaka wa kusan mutane 10,000, musamman marayu, domin su samu damar gudanar da bikin Sallah cikin farin ciki. Ya bayyana cewa tallafin wani ɓangare ne na ƙoƙarin taimaka wa marasa galihu musamman a cikin watan Ramadan da lokacin Sallah. A nasa jawabin, shugaban hukumar SOZEA, Lawal Maidoki, ya gode wa sanatan kan wannan taimako, yana mai cewa za a raba tallafin yadda ya dace ga waɗanda aka nufa da shi.

Nuri-Tilawah International School Zaria Hosts Ramadan Iftar Under Saudi Programme

Image
Nuri-Tilawah International School, Zaria, under the leadership of Sheikh Dr. Nuraddeen Umar Tahir, has been hosting a Ramadan Iftar gathering as part of a programme supported under the initiative of the Custodian of the Two Holy Mosques, King Salman bin Abdulaziz Al-Saud. The Iftar programme, which began on the 20th day of Ramadan, is bringing together members of the community, scholars and guests for collective prayers and reflection during the holy month. The programme is implemented under the supervision of the Saudi Ministry of Islamic Affairs, Da’wah and Guidance, and is being held at Nurul Tilawah International School, Tukur-Tukur Layout, Zaria, Kaduna State. Speaking during the Iftar held on the 24th day of Ramadan, the Director of the school, Sheikh Dr. Nuraddeen Umar Tahir, explained that the gathering was organised to strengthen unity among Muslims and encourage spiritual devotion during Ramadan. He noted that Nuri-Tilawah International School is one o...

ADC Chieftain Urges Continued Support for Party in Zaria

Image
A chieftain of the African Democratic Congress (ADC) in Zaria Local Government Area of Kaduna State, Hon. Bashir, has called on members and supporters of the party to remain committed and continue to give their full support toward strengthening the party ahead of future political activities. Hon. Bashir made the call while speaking with journalists in Zaria, where he emphasized the need for unity and collective effort among members to ensure the growth and success of the party at all levels. He also urged members of the public, particularly eligible citizens, to come forward and register as members of the African Democratic Congress (ADC), noting that expanding the party’s membership base is crucial for building a strong and credible political platform. Commenting on recent developments involving the detention of former Kaduna State Governor, Malam Nasir El-Rufai, by the Independent Corrupt Practices and Other Related Offences Commission (ICPC) and the Economic and Financia...

Bashir Umar: Ku Fito Ku Yi Rajista da ADC Domin Sauya Siyasar Najeriya

Image
Daga Muazu Abubakar Albarkawa  Wani jigo a jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a ƙaramar hukumar Zaria ta Jihar Kaduna, Hon. Bashir Umar, ya yi kira ga mambobi da magoya bayan jam’iyyar da su ci gaba da bai wa jam’iyyar haɗin kai da goyon baya domin ƙarfafa ta a matakai daban-daban. Hon. Bashir ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da manema labarai a Zaria, inda ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin mambobin jam’iyyar domin tabbatar da cigaban ta da kuma samun nasara a harkokin siyasa a nan gaba. Ya kuma yi kira ga al’umma, musamman masu cancantar shiga siyasa, da su fito su yi rajista da jam’iyyar ADC, yana mai cewa faɗaɗa yawan mambobin jam’iyyar na daga cikin matakan da za su taimaka wajen gina jam’iyya mai ƙarfi da tasiri a ƙasar nan. Dangane da batun da ya shafi tsare tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da hukumomin ICPC da EFCC ke yi, Hon. Bashir Umar ya ce ya kamata a gudanar da lamarin cikin adalci da kuma bin doka da oda. A cewarsa, y...

Dangote ya rage farashin man fetur

Image
Matatar man Dangote ta sanar da rage farashin man fetur daga naira 1,175 kan kowace lita zuwa naira 1,075 wato ragin naira 100 kenan. Wata sanarwa da matatar ta fitar a shafinta na X ta bayyana cewa matakin ya biyo bayan saukar farashin danyen mai a kasuwannin duniya kuma anyi hakan ne bisa tsarin sabon farashi da kamfanin ya fitar. Sanarwar ta kuma bayyana cewa matatar ta rage farashin man dizal zuwa naira 1,430 kan kowace lita daga tsohon farashin naira 1,620. Matatar ta jaddada ƙudurinta na taimakawa wajen karfafa tsaron makamashi a Najeriya tare da la’akari da halin tattalin arzikin da ‘yan kasar ke ciki in ji babban jami'in. Wannan shi ne karo na farko da aka rage farashin bayan ƙarin sau uku a jere da aka yi a makonnin baya wanda ya sa farashin man ya yi matukar tashi.

Iran ta kai 'hari mafi muni' kan Isra'ila da sansanonin sojin Amurka

Image
Iran ta ƙaddamar da hare-haren makamai masu linzami kan wasu sansanonin sojin Amurka da ke Gabas ta Tsakiya, kamar yadda wata sanarwa daga rundunar juyin juya halin Iran ta bayyana a shafin X. Sanarwar ta ce an harba makamai zuwa sansanin Al Udeid da ke Qatar, da sansanin Arifjan a Kuwait, da kuma sansanin Harir a Iraƙi. Kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Iran, ISNA, ya ce harin mai yawa da aka ƙaddamar ya kuma nufi rundunar ruwa ta biyar ta Amurka da ke yankin, inda aka ce wasu muhimman kayayyakin aikin sojojin Amurka sun lalace. A wani sako na daban, an bayyana harin a matsayin mafi girma kuma mafi muni da Iran ta kai tun bayan fara wannan rikici. Sai dai zuwa yanzu jami’an Amurka ba su fitar da wata sanarwa ba kan lamarin. A lokaci guda kuma an ji kuwwar na’urorin gargadi a sassa da dama na Isra’ila bayan wani sabon harin makamai masu linzami da Iran ta kai, wanda gidan talabijin na Isra’ila ya bayyana a matsayin mafi muni tun soma yakin. Isra’ila ta ce garkuwar tsa...

Gwamnatin jihar Jigawa ta kara alawus din masu unguwanni daga N3,000 zuwa N10,000

Image
Gwamnan Umar Namadi na jihar Jigawa ya amince da ƙara alawus ɗin da ake bai wa masu unguwa na wata-wata daga naira dubu uku zuwa naira dubu goma. An sanar da wannan mataki ne bayan zaman majalisar zartarwar jiha da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Dutse a ranar Talata. Da yake yi wa manema labarai bayani kan sakamakon zaman, kwamishinan muhalli da sauyin yanayi na jiha, Dr. Nura Kazaure, ya ce karin alawus ɗin na nuna kulawa da tausayi da gwamnatin gwamnan ke nunawa shugabannin gargajiya na matakin ƙasa. An dauki matakin ne, duba da halin da tattalin arziki ke ciki da kuma nauyin da shugabannin gargajiya ke ɗauka wajen hidimar al’umma.

Sallar Juma'a ta gagari kauyuka kusan 10 a jihar Katsina ta dalilin ayyukan barayin daji

Image
Fargaba ta mamaye wasu kauyuka a jihar Katsina bayan wani mummunan rikici tsakanin kungiyoyin ‘yan bindiga da ya tilasta wa mazauna sama da kauyuka goma dakatar da sallar Juma’a saboda tsananin harbe-harben bindiga da ya dauki tsawon sa’o’i. Manema labarai  sun ruwaito cewa rikicin ya faru ne a yankunan karkara da ke iyaka da kananan hukumomin Musawa, Kankara da kuma Malumfashi, inda aka yi musayar wuta tsakanin kungiyoyin ‘yan bindiga na tsawon lokaci, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin tsananin fargaba. Rahotanni sun ce tun kafin lokacin sallar Juma’a, wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kai farmaki a garin Dangani da rana tsaka, inda suka shiga garin kan babura fiye da 70. Maharan sun lalata shagunan sayar da wayoyi tare da kwace wayoyin da ake cajawa a wuraren caji da kuma wadanda suka samu a hannun mazauna yankin.

2027: PDP Will Overcome Internal Crisis, Remain Strong Opposition – MBY

Image
By Muazu Abubakar Albarkawa  A chieftain of the Peoples Democratic Party (PDP) and close associate of the party’s national leader, Barrister Kabir Tanimu Turaki, Hon. Muttaka Balarabe Yakub (MBY), has alleged that the lingering crisis within the opposition party is being fueled by individuals who are receiving backing from the ruling All Progressives Congress (APC). Speaking with journalists in Abuja, MBY said the internal disputes currently affecting the PDP are not organic disagreements within the party but are being orchestrated by certain individuals working in the interest of the ruling party. According to him, “The truth is that some of the crises being witnessed in the PDP today are sponsored by people who are enjoying the support of the APC-led government. Their aim is to weaken the only opposition platform capable of challenging the ruling party in the country.” Muttaka Yakub specifically cited the Minister of the Federal Capital Territory, Nyesom Wike, and for...

Rundunar tsaro ta Civil Defence za ta tura dakaru 11,000 da za su ba da kariya ga manoma a Daminar 2026

Image
Hukumar tsaron Civil Defence (NSCDC) ta bayyana shirin tura jami’an ta na Agro-Rangers sama da dubu goma sha daya domin kare manoma a fadin Najeriya yayin da ake shirin fara kakar noma ta shekarar 2026. Mai magana da yawun hukumar, Babawale Afolabi, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da jaridar Sunday Punch, inda ya ce hukumar na daukar matakai masu karfi domin tabbatar da tsaron manoma da kuma kare harkokin noma a kasar. A cewarsa, shugaban hukumar NSCDC, Abubakar Audi, ya sake jaddada kudurin hukumar na tura jami’an da aka horar musamman zuwa wuraren noma domin kare rayukan manoma da dukiyar da ta shafi noma. Matakin na zuwa ne bayan jerin hare-hare da suka faru kan manoma a wasu sassan Najeriya a shekarar 2025.

Akwai yiyuwar mutum 2 sun rasa rayukansu a rikicin kabilanci a jihar Adamawa

Image
Rahotanni daga jihar Adamawa na cewa mutum biyu sun rasa rayukansu a sabon rikicin da ya tashi tsakanin al’ummomin Chobo da Bachaman a karamar hukumar Lamurde, ta jihar. Mai magana da yawun ‘yan sanda na jihar, Suleiman Yahaya-Nguroje, ya ce rikicin ya barke ne a daren Asabar bayan wasu matasan Chobo sun farmaki garin Lamurde, inda suka yi harbi, abin da ya sa matasan Bachaman suka yi ramuwar gayya. An ruwaito cewa an tura jami’an ‘yan sanda domin dawo da zaman lafiya, yayin da ake ci gaba da tattara rahotannin hasarar rayuka. Wannan rikici wanda ya samo asali ne a kan rikicin kasa a yankin, wanda a cikin watanni shida da suka gabata ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 30, musamman mata.

Sojojin Najeriya sun kuɓutar da mutum 19 da aka sace a Abuja

Image
Jami'an tsaron Najeriya sun ce sun kuɓutar da mutum 19 da aka yi garkuwa da su a Abuja, babban birnin ƙasar. Cikin wata sanarwa da sojojin ƙasar suka fitar ranar Asabar, sun ce sun kubutar da mutanen a lokacin wani samamen hadin gwiwar jami'an tsaron ƙasar a ƙauyen Gidan Dogo da ke yankin ƙaramar hukumar Bwari. Sanarwar ta ce jami'an suin kai samamen ne bayan samun bayanan sirri kan maɓoyar ƴanbindigar da suka sace mutanen. Sojojin sun ce an kashe mutum ɗaya cikin wadanda ake zargi da satar mutanen, yayin da sauran suka gudu, wasu da raunuka. Satar mutanen domin neman kudin fansa na ci gaba da yawaita a ƴan shekarun nan a Najeriya, inda ƴanbindigar ke far wa garuruwa da tare kan manyan tituna domin satar mutane. Duk da cewa a baya matsalar ta fi yawa yankin arewa maso yammcin ƙasar, a baya-bayan nan ta yi naso zuwa Abuja, babban birnin ƙasar.

Matashi daga jihar Kano ya ƙaddamar da takarar kujerar shugaban matasa na jam'iyyar APC na ƙasa

Image
Wani dan jam’iyyar APC, Bashir Suwaid, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Shugaban Matasan jam’iyyar na kasa. Suwaid, wanda dan asalin jihar Kano ne, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, inda ya ce ya dauki matakin ne bayan tuntuba da shugabannin jam’iyya da masu ruwa da tsaki na matasa a fadin kasar. Da yake jawabi ga shugabannin jam’iyya da ‘yan jarida, Suwaid ya ce ya zama dole a kara karfafa bangaren matasan APC tare da inganta tsarinsa domin amfani da karfi da gudunmawar matasa a duk fadin kasar. Ya ce matasan jam’iyyar sun taka muhimmiyar rawa wajen tattara goyon baya da kuma karfafa tsarin jam’iyyar tun daga matakin mazabu har zuwa kasa baki daya. Suwaid ya kuma jaddada cewa matasan Nijeriya a yanzu sun fi ilimi da hadin kai, kuma suna da sha’awar ba da gudunmawa ga ci gaban kasa. Ya kara da cewa ya shiga takarar ne cikin kaskantar da kai tare da girmama sauran masu neman kujerar, yana mai alkawarin yi wa jam’iyyar aiki da g...

Trump ya ce ba ya neman taimakon Birtaniya a yaƙin Iran

Image
A wani mataki na nuna fushinsa, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ƙasarsa ba ta buƙatar taimakon Birtaniya a yaƙin da take yi a Iran. Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Shugaba Trump ya ce Amurka ba ta buƙatar manyan jiragen dakon kaya na Birtaniya biyu a Gabas ta Tsakiya. "Birtaniya, ɗaya daga cikin manyan ƙawayenmu, watakila ma babba cikin ƙawayen namu, a yanzu na nuna shakku kan tura manyan jiragensu biyu zuwa Gabas ta Tsakiya. Amma ba komai'', kamar yadda ya wallafa. ''Amma firministan Birtnaiya ka sanin mu yanzu ma ba ma buƙatarsu - Amma za mu riƙa tuna wannan. Mu ba ma son ma mutane su shigar mana yaƙi bayan mun riga mnun yi nasara''. Wanna na zuwa ne bayan Staemer ya ƙi amincewa Amurka ta yi amfani da sansanonin sojin Birtaniya a yankin Gabas ta Tsakiya don kai wa Iran hare-hae. Daga baya Trump ya ce ''Ba ya son taimaka mana''. “Ban taɓa tsammanin haka ba, ban taɓa tsammanin Birtaniya za ta yi mana ...

Gwamna Abba Gida Gida ya ƙaddamar da rabon buhunan shinkafa 100,000 na gidauniyar Dangote

Image
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da rabon buhunan shinkafa 100,000 da gidauniyar Aliko Dangote ta bayar domin tallafa wa marasa karfi a jihar. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Mustapha Muhammad, ya fitar a Kano, gwamnan ya gode wa gidauniyar bisa wannan tallafi, yana mai cewa ya zo a daidai lokaci musamman a watan Ramadan. Yusuf ya tabbatar da cewa za a raba tallafin cikin gaskiya da adalci ta hanyar shugabannin al’umma da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa ya kai ga waɗanda aka nufa da shi. Shi ma kwamishinan noma da albarkatun ƙasa na jihar, Dakta Danjuma Mahmud, ya yaba wa gidauniyar Dangote kan ba gwamnatin jihar damar kula da rabon tallafin kai tsaye.

NDLEA ta kama wani tsohon Kansila a Legas da tabar wiwi kilo 40

Image
Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya, NDLEA, ta kama Sheleru Sadiq, tsohon kansila a yankin Orimedu da ke ƙaramar hukumar Ibeju-Lekki a jihar Lagos , bisa zargin mallakar wiwi kilo 40. Mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ya ce an kama Sadiq a gidansa a ranar 2 ga Maris, inda jami’an suka gano wiwi nau’in skunk kilo 40 a ɗaya daga cikin ɗakunan gidan. Ya kuma amsa cewa kayan da gidan nasa ne. A cewar NDLEA, Sadiq wanda a yanzu yake aiki a matsayin mataimakin majalisa, ya taɓa yin wa’adin kansila sau biyu yana wakiltar al’ummar Orimedu. A wani samame dabam, jami’an NDLEA sun kuma kama Emeka Hyginus Okwor da ƙwayoyi 1,000 na tapentadol da aka ɓoye a cikin pampers na jarirai, yayin da aka kama wani ɗan Kamaru, Mey Ali Muhamat, da miyagun ƙwayoyi a jihar Kogi . Haka kuma jami’an sun kama Osama Abdullahi a jihar Niger bayan gano sassan na’urar fashewa (IED) guda 500 a cikin wata motar haya. Bugu da ƙari, jami’an sun ƙwato ƙwayoyin tramadol 122,000 d...

Iyalan El-Rufai sun buƙaci a sake shi ba tare da ɓata lokaci ba

Image
Iyalan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai sun bayyana cigaba da riƙe shi da ake yi a matsayin karan-tsaye ga dokokin Najeriya, sannan suka yi zargin ana amfani da hukumar yaƙi da cin hanci a matsayin karen farauta domin muzgunawa ƴan hamayya. Iyalan sun bayyana haka ne a wata sanarwa da Bello El-Rufai ya fitar a madadinsu a ranar Juma'a, 6 ga watan Maris, inda ya bayyana tsare mahaifin nasu da "saɓa doka." "Har yau Juma'a 6 ga watan Maris, Nasir El-Rufai na tsare a hannun ICPC wanda ba bisa doron doka suke yi ba. Muna sanar da al'umma cewa babu dokar da ta amince a cigaba da tsare shi." Iyalan sun ce an fara tsare tsohon gwamnan ne a ranar 18 ga Fabrairun 2026, "sannan hukumar ta nemi izinin tsare shi na kwana 14. Amma har yanzu da kwanakin suka ƙare, ICPC ba ta kai shi kotu ba, sannan tana cigaba da tsare shi. Wannan karan-tsaye ne ga dokokin Najeriya, saboda hukumar ta gaza wajen gabatar da shi a kotu, ko kuma ta sake shi....

Majalisa ta gayyaci Kyari kan zargin ɓatan maƙudan kuɗi a NNPCL

Image
Kwamitin kula da asusun gwamnati na Majalisar Dattawan Najeriya ya gayyaci tsohon shugaban Kamfanin Man Fetur na ƙasar, Mele Kyari, domin ya yi bayani kan zargin wasu kuɗaɗe da yawansu ya kai naira tiriliyan 210 da ake cewa ba a yi cikakken bayanin yadda aka kashe su ba tsakanin shekarun 2017 zuwa 2023, lokacin da yake jagorantar kamfanin. An gayyaci Kyari tare da tsohon babban jami’in kula da harkokin kuɗi na kamfanin, Umar Ajia Isa, da kuma tsohon babban manajan kula da harkokin zuba jari na kamfanin, Bala Wunti. Shugaban kwamitin, Sanata Aliyu Wadada, ne ya bayar da umarnin gayyatar a ranar Alhamis bayan da kwamitin ya duba rahotannin binciken kuɗi da suka shafi kamfanin NNPCL. Kwamitin ya kuma yi gargaɗin cewa zai iya fitar da sammacin kama waɗanda abin ya shafa idan suka gaza bayyana a gaban kwamitin a ranar da za a sanar nan gaba. Sanata Wadada ya bayyana wannan matsaya ta kwamitin ne yayin da yake yi wa manema labarai ƙarin bayani bayan kammala taron kwamitin. A cewa...

Gwamnatin Jigawa ta sallami ‘yan kwangila 22 kan zargin almundahana a shirin ciyarwar Ramadan

Image
Gwamnatin Jihar Jigawa ta sallami ‘yan kwangila da kamfanoni 22 da ke gudanar da shirin ciyar da jama’a abincin buda baki a watan Ramadan, bayan zargin magudi, rashin ingancin abinci da kuma almundahanar kudade. Kwamishinan Ma’aikatar Jin Kai da Ayyuka na Musamman ta jihar, Auwalu Sankara, ya bayyana haka a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Dutse ranar Juma’a. Ya ce an dauki matakin ne bayan rahotannin sa ido da korafe-korafen jama’a da suka nuna cewa wasu daga cikin ‘yan kwangilar na bada abinci mara inganci, rage adadin abinci, da kuma tafiyar da kudaden shirin ba bisa ka’ida ba. Shirin ciyarwar, wanda gwamnan jihar Umar Namadi ya kaddamar, na da nufin ciyar da mutane kimanin miliyan 7.9 a cibiyoyi 640 a fadin jihar domin tallafawa marasa karfi a watan Ramadan na 2026. Sankara ya ce gwamnati ba za ta lamunci duk wani aiki da zai bata manufar shirin jin kai na gwamnatin jihar ba, yana mai jaddada cewa an fara daukar sabbin ‘yan kwangila domin maye gurbin wadanda ...

Da yiwuwar farashin gangar mai ya kai $150 nan da kwanaki uku — Ministan makamashi na Qatar

Image
Ministan makamashi na ƙasar Qatar, Saad Al‑Kaabi, ya yi gargadin cewa farashin ɗanyen mai na duniya na iya kaiwa dala 150 a kowace ganga cikin makonni biyu zuwa uku idan jiragen dakon mai suka ci gaba da kasa wucewa ta mashigin ruwa na Strait of Hormuz. Al-Kaabi ya bayyana haka ne a wata hira da jaridar Financial Times, inda ya ce rikicin da ake yi tsakanin Iran da ƙawayen Amurka da Israel ya haifar da barazanar tsaro a yankin, lamarin da ya sa wasu manyan kamfanonin jigilar kaya suka dakatar da zirga-zirga ta mashigin Hormuz da kuma Suez Canal. Ya ce idan wannan matsala ta ci gaba, kasuwar makamashi ta duniya za ta fuskanci matsananciyar tangarda, inda kuma farashin iskar gas zai iya tashi har zuwa dala 40 a kowace MMBtu. Ministan ya kuma ce kamfanonin mai na yankin Tekun Fasha na iya ayyana force majeure, wanda zai sa su dakatar da fitar da makamashi zuwa kasuwannin duniya. A wani bangare kuma, kamfanin makamashi na gwamnati QatarEnergy ya dakatar da samar da iskar gas ma...

Gwamna Radda ya bada zakkar Naira miliyan 50 daga dukiyar sa zuwa hukumar Zakka da Waƙafi ta Jihar Katsina

Image
Gwamnan Jihar Katsina, Dr. Dikko Umaru Radda PhD. ya Kaddamar da bada Naira miliyan 50 na wani sashe daga cikin zakkarsa, wanda ya baiwa Hukumar Zakka da Waqafi ta Jihar Katsina. Yayin da ya ke kaddamarwa ya bayyana cewa tunda ya fara fitar da zakka dukiyarsa ke karuwa. Ya kuma bayyana irin alkairan da fitar da Zakka ke kawo ga al'umma wanda hakan ya sanya Gwamnatinsa ta kafa Hukumar Zakka da Waqafi.  A na shi Jawabin Shugaban Gammayar Kungiyoyin Zakka da Wakafi ta Nigeria, kuma Mataimakin Sakatare na Zakka da Wakafi ta duniya Engr. Muhammad Lawal Maidoki ya bayyana Gwamnan jihar Katsina a matsayin abin koyi wanda yake fitar da hakkin Allah. A na shi Jawabin Shugaban Hukumar Zakka da Wakafi Dr. Ahmad Musa Abdullahi ya bayyana yadda Mai Girma Gwamna ya ke ba Hukumar cikakken goyon baya tun daga sadda a ka kafa hukumar. Cikin wanda suka kaddamar da ta su Zakkar akwai Mai Girma Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Mallam Faruk Lawal Jobe (Sarkin Fulani Joben Katsina), Mai Girm...

Gwamna Dauda Lawal ya zamanantar da tsarin tattara kuɗin shiga a Zamfara daga biyan kuɗi hannu zuwa ta intanet

Image
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da karɓar duk wani kuɗin shiga na gwamnati ta hanyar tsabar kuɗi a faɗin jihar, domin ƙarfafa tsarin dijital, daidaita bayanan ma’aikatu da hukumomi, ba da damar sa ido kai tsaye, da kuma rage asarar kuɗaɗen shiga. Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wani taron wayar da kai kan Dokokin Gyaran Haraji na Nijeriya 2025, wanda Hukumar Tara Haraji ta Jihar Zamfara ta shirya a Gusau. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, gwamnan ya bayyana cewa burin jihar na tara kuɗaɗen shiga na cikin gida (IGR) na shekarar 2026 tsakanin naira biliyan 38 zuwa 42 ya ta’allaka ne kan sabbin gyare-gyaren da aka fara aiwatarwa da kuma faɗaɗa tsarin bin doka.

PDP ce kaɗai jam’iyyar adawa a Nijeriya yanzu – Wike

Image
Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa jam’iyyar adawa kaɗai da ya sani a halin yanzu a Nijeriya ita ce PDP. Wike ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai, inda ya ce sauran jam’iyyun siyasa ba su da tasiri a zahiri a fagen adawa a ƙasar. A cewarsa, PDP ce kaɗai ke nuna ƙarfin adawa ga manufofin gwamnati, yayin da APC ke riƙe da madafun iko a matakin tarayya.

An karrama Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da lambar yabo ta “Gwamnan Shekara ta 2025”

Image
An karrama Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da lambar yabo ta “Gwamnan Shekara ta 2025”daga Silverbird Group, a wani taro da aka gudanar a Eko Hotels and Suites, Victoria Island, a ranar Lahadi. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar manema labarai da Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan Kano, Mustapha Muhammad, ya fitar. A cewar masu shirya taron, an ba gwamnan wannan lambar yabo ne sakamakon irin kokarinsa wajen tabbatar da shugabanci nagari da kuma aiwatar da manufofi da ayyukan raya kasa da suka shafi rayuwar al’umma kai tsaye. Sanarwar ta ce tun bayan fara wannan gwamnati, an samu sauye-sauye a fannoni daban-daban da suka hada da ilimi, kiwon lafiya, gine-gine da ababen more rayuwa, da kuma bunkasa harkar noma. Masu shirya taron sun kuma bayyana gwamnan a matsayin jagora mai hangen nesa wanda ke kokarin daukaka martabar jihar Kano, tare da jaddada cewa shirin “Kano First Agenda” ya kara karfafa tafiyar ci gaban jihar. Sai dai gwamnan bai samu damar halartar taron...

Najeriya za ta karɓi maganin rigakafin HIV a watan Maris – NACA

Image
Hukumar dakile yaduwar cuta mai karya garkuwar jiki (NACA) ta sanar da cewa Najeriya za ta karɓi maganin rigakafin cutar HIV mai suna Lenacapavir a watan Maris 2026. A cikin wata gajeriyar sanarwa da Shugabar Hulɗa da Jama’a ta hukumar, Toyin Aderibigbe, ta fitar a ranar Litinin, ta bayyana cewa hukumar ta samu amincewar doka daga hukumar NAFDAC domin shigo da maganin cikin ƙasa. Lenacapavir magani ne da ake yi ta allura sau biyu kacal a shekara, wanda hakan ya sa ya fi sauƙi idan aka kwatanta da magungunan rigakafin da ake sha kullum. Gwaje-gwajen kimiyya sun nuna cewa maganin ya nuna kashi 100 cikin 100 na kariya daga kamuwa da cutar HIV a binciken asibiti. Sanarwar ta ce gwamnatin Najeriya na ci gaba da shirye-shiryen fara amfani da maganin a matsayin rigakafin kafin kamuwa da cuta (PrEP), a wani ɓangare na ƙudurin gwamnati na ƙarfafa yaƙi da HIV da kuma hanzarta rage yaduwar cutar a ƙasa. Hukumar ta kuma bayyana cewa ana sa ran maganin zai kasance a Najeriya da wasu ƙas...

Jiragen yaƙi da dama na Amurka sun yi hatsari a Kuwait - Ma'aikatar tsaro

Image
Ma’aikatar Tsaro ta ƙasar Kuwait ta sanar da cewa jiragen yaƙi da dama na rundunar sojin Amurka sun yi haɗari a safiyar yau a ƙasar da ke gabas ta tsakiya kamar yadda jaridar TheCable ta wallafa. Har yanzu ba a san abin da ya haddasa haɗarin ba, amma kakakin ma’aikatar tsaron ya tabbatar a cikin wata sanarwa cewa ma’aikatan jiragen sun tsira gaba ɗaya ba tare da wata matsala ba. Ba a kuma bayyana adadin jiragen yaƙin ko yawan ma’aikatan da abin ya shafa ba. A cewar sanarwar, jami’an tsaro sun kwashe ma’aikatan jiragen tare da kai su asibiti domin kula da lafiyarsu bayan an kammala aikin ceto da bincike. Sanarwar ta bayyana cewa yanayin lafiyar ma’aikatan “yana da kyau kuma yana da daidaito.” “Jami’an da abin ya shafa na ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin,” in ji sanarwar. Tun da fari, wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta ya nuna wani jirgin yaƙi yana cin wuta kafin ya faɗi a sararin samaniyar Kuwait, kusa da wani sansanin sojin Amur...

Hisbah ta yi barazanar gurfanar da masu tashe a kotu

Image
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta yi barazanar kai duk wanda aka kama yana gudanar da tashe zuwa kotu, sakamakon yadda wasu ke amfani da al’adar wajen aikata laifuka da tayar da hankalin jama’a. A wata sanarwa da Mataimakin Babban Kwamandan hukumar, Dakta Mujahiddin Aminuddin, ya fitar, ya ce wasu bata-gari na amfani da tashe wajen yin sare-sare, doke-doke da cin mutuncin mutane, a wasu lokuta har da firgita al’umma. Ya tunatar da jama’a cewa watan Ramadan lokaci ne na ibada, istigfari, tuba, rahama da kuma ‘yantar da bayi daga wuta. Ya kara da cewa bai dace a rika amfani da sunan Musulunci ko addini wajen cin mutunci ko cin zarafin wani ba, domin hakan ya sabawa koyarwar addini. Dakta Aminuddin ya yi kira ga al’umma da su bi doka tare da guje wa duk wani abu da zai iya kawo hargitsi. Ya kuma gargadi cewa duk wanda hukumar ta kama da hannu a irin wadannan ayyuka, za a gurfanar da shi a kotu domin ya fuskanci hukunci daidai da laifin da ya aikata.

Tiani ya karɓi rahoton bincike kan illar hakar Uranium a Arlit

Image
Shugaban mulkin sojin Jamhuriyar Nijar, Janar Abdurahamane Tiani, ya karɓi binciken kwamitin ƙwararrun masana da aka kafa domin binciken tasirin ayyukan hakar uranium a yankin Arlit, a ranar 28 ga Fabrairu, 2026. Bayan fiye da shekara ɗaya da rabi ana gudanar da binciken, kwamitin ya miƙa taƙaitaccen rahoton sakamakon bincikensa ga shugaban. A cewar mai ba Shugaban shawara na musamman, sakamakon binciken ya nuna cewa ayyukan kamfanin Orano da suka shafe fiye da shekaru 50 a yankin sun bar manyan matsaloli masu tsanani, musamman ga tsarin halittu da kuma muhalli gaba ɗaya.

Mutane 3 da za su jagoranci Iran bayan rasuwar jagoran jamhuriyar musulunci, Ayatollah Ali Khamenei

Image
Kwamitin mutune uku zai jagoranci ƙasar Iran na wucin gadi bayan rasuwar Jagoran Jamhuriyar Musulunci, Ayatollah Ali Khamenei. Rahotanni daga kafafen yaɗa labarai na gwamnatin Iran sun bayyana cewa kwamitin zai ƙunshi Shugaban Ƙasa, Masoud Pezeshkian, shugaban ɓangaren shari’a, Gholamhossein Mohseni Ejei, da kuma wani mamba daga Majalisar Masu Tsaron Tsarin Mulki (Guardian Council). Za su riƙe ragamar mulki a lokacin miƙa mulki. Mutanen uku za su karɓi ayyukan marigayi Khamenei har sai Majalisar Kwararru (Assembly of Experts), wadda ta ƙunshi manyan malamai 88 masu tasiri, ta zaɓi sabon jagora. Dokar ƙasar Iran ta tanadi cewa Majalisar Kwararru dole ne ta zaɓi sabon Jagoran Koli cikin gaggawa. Har yanzu ba a bayyana wanda zai gaji Khamenei ba, wanda aka kashe a hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran a ranar Asabar.