Posts

Showing posts from April, 2026

Yusuf Maitama Tuggar: Experience, Vision, and a Defining Moment for Bauchi State

Image
The race toward the 2027 governorship election in Bauchi State has taken a compelling turn with the emergence of former Minister of Foreign Affairs, Yusuf Maitama Tuggar, as a leading and formidable contender. With a rich blend of diplomatic experience, legislative background, and deep grassroots connection, Tuggar’s candidacy is fast becoming a symbol of hope, renewal, and purposeful leadership. Born on March 12, 1967, into a politically conscious family in Gamawa, Tuggar’s journey into leadership appears almost destined. His father, Abubakar Tuggar, was a respected political figure during Nigeria’s First Republic, laying a foundation of public service that has clearly influenced his path. From an early age, Tuggar was exposed to the values of leadership, responsibility, and national service principles that continue to define his career. Academically, Tuggar stands out as a man of intellect and global exposure. With a degree in international relations, further studies at t...

Tinubu ya rantsar da Muttaqha Darma a matsayin ministan gidaje

Image
Tinubu ya rantsar da Muttaqha Darma a matsayin ministan gidaje Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Dr. Muttaqha Rabe Darma a matsayin Ministan Gidaje da Raya Birane, bayan amincewar majalisar dattawa. Darma ya maye gurbin Ahmed Musa Dangiwa da ya yi murabus kwanan nan. A wajen bikin rantsarwar da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Abuja, Tinubu ya bayyana cewa nadin ya zo ne a wani muhimmin lokaci na ci gaban ƙasa, yana mai jaddada cewa ana buƙatar ƙwararrun mutane domin tafiyar da harkokin gwamnati. Sabon ministan ƙwararre ne a fannin gudanarwa da ci gaba, inda ya yi karatu a Jami'ar Bayero Kano da kuma wasu jami’o’i na ƙasashen waje. Ya taɓa riƙe mukamai da dama a jihar Katsina, ciki har da kwamishinan ayyuka da na raya karkara. Sanarwar rantsarwar ta fito ne daga bakin mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga.

Dakarun sojin Nijeriya sun kashe 'yan ta’adda 24 a Yobe

Image
Dakarun sojin Nijeriya sun kashe 'yan ta’adda 24 a Yobe Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Gabas, Operation Hadin Kai, sun dakile wani hari da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka kai a garin Kukareta da ke jihar Yobe , inda suka kashe mutum 24 daga cikin maharan bayan fafatawa mai tsanani. Rahotanni sun ce harin ya faru ne da sanyin safiyar Alhamis, inda maharan suka yi ƙoƙarin kwace sansanin sojoji da ke yankin. Fafatawar ta ɗauki kusan awa uku kafin sojojin su samu nasarar murƙushe harin. Jami’in yaɗa labarai na rundunar, Sani Uba, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce sojojin sun mayar da martani cikin gaggawa tun bayan fara harin daga tsakar dare zuwa kusan ƙarfe 3 na safe. Ya ƙara da cewa dakarun sun haɗa kai wajen kai farmaki da kare kansu a lokaci guda, abin da ya tilasta maharan ja da baya cikin ruɗani. A cewarsa, an kashe ‘yan ta’adda 24 yayin artabun, sannan sojojin sun kwato makamai masu yawa daga hannunsu. Daga cikin k...

Gwamnatin tarayya na shirin sassauta bashin kamfanonin jiragen sama

Image
Gwamnatin tarayya na shirin sassauta bashin kamfanonin jiragen sama Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin rage ko ma yafewa kamfanonin jiragen sama wasu daga cikin basussukan da suke bin hukumomin kula da harkokin jiragen sama, domin rage musu nauyin da suka shiga sakamakon tashin farashin man jirgi (Jet A1). Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya ce Shugaban ƙasa na duba yiwuwar ba da rangwame kan basussukan da hukumomi kamar Hukumar Kula da Sararin Samaniya (NAMA), Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Tarayya (FAAN) da kuma Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) suke bin kamfanonin. Ya ƙara da cewa za a kafa wani kwamiti na musamman da zai duba haraji da kudaden da ake ɗora wa tikitin jiragen sama na cikin gida, domin rage tsadar sufuri ga ‘yan ƙasa. A nasa ɓangaren, shugaban kamfanin jiragen sama na Air Peace, Allen Onyema, ya bayyana cewa matsalar da kamfanonin ke fuskanta ta samo asali ne daga hauhawar farashin man Jet A1, wanda ya ƙaru da sama da kashi 300...

Majalisar Dattawa ta nemi a ɗauki matakin gaggawa kan tsaro a jihohin Arewa

Image
Majalisar Dattawa ta nemi a ɗauki matakin gaggawa kan tsaro a jihohin Arewa Majalisar dattawa ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakan gaggawa domin magance matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara, ciki har da yiwuwar dakatar da harkokin siyasa a wasu jihohin Arewa guda takwas da abin ya fi shafa. Jihohin da aka ambata sun haɗa da Borno, Plateau, Bauchi, Benue, Niger, Sokoto, Kebbi da wasu sassan Kano, inda ake fama da hare-haren ‘yan ta’adda da rashin tsaro. Wannan kira ya biyo bayan ƙorafin Sanata Abdul Ningi, wanda ya bayyana cewa matsalar tsaro na ƙaruwa, yana mai jaddada cewa lokaci ya yi da gwamnati za ta daina yin shiru tare da ɗaukar mataki mai ma’ana. Majalisar ta kuma buƙaci a ƙara ƙaimi wajen ceto mutane 416 da ake zargin ƙungiyar Boko Haram ta sace a jihar Borno, waɗanda suka haɗa da mata, yara da tsofaffi. Sanatocin sun nuna matuƙar damuwa kan yadda ake kai sabbin hare-hare kan sansanonin sojoji, suna mai cewa hakan na barazana ga tsaron ƙasa baki ɗaya. Sun...

DA DUMI-DUMI: Majalisar dokokin jihar Kano ta tantance Murtala Sule Garo don zama mataimakin Gwamna

Image
DA DUMI-DUMI: Majalisar dokokin jihar Kano ta tantance Murtala Sule Garo don zama mataimakin Gwamna  Majalisar dokokin jihar Kano ta kammala tantance Hon. Murtala Sule Garo, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa a matsayin Mataimakin Gwamna. Sakataren yaɗa labarai na majalisar dokokin jihar Kano, Kamaludeen Sani Shawai ne ya tabbatar da hakan cikin wata gajeriyar sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook. Acewarsa, kwamitin da Mataimakin Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Muhammad Bello Butu Butu ke jagoranta, zai gabatar da rahotonsa ranar Litinin domin amincewa ta ƙarshe.

DSS ta gurfanar da El-Rufai a kotu kan zargin naɗar kiran wayar Ribadu ba bisa ƙa'ida ba

Image
DSS ta gurfanar da El-Rufai a kotu kan zargin naɗar kiran wayar Ribadu ba bisa ƙa'ida ba Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, bisa zargin kutsawa cikin tattaunawar wayar mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu. Jaridar TheCable ta rawaito cewa an tuhumi El-Rufai da laifuka biyar bayan an yi wa tuhumar gyara daga uku zuwa biyar. Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta soke tsohuwar tuhumar tare da ci gaba da sauraron sabuwar. El-Rufai ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake masa. Bayan haka, lauyansa ya bukaci a ba shi damar tattaunawa da wanda yake karewa, yana mai cewa yana hannun hukumomin tsaro daban-daban. Sai dai alkalin kotun ta ce ba ta ga karin bayanin da aka ce an shigar ba, inda ta bukaci lauyan ya bi ka’idojin shigar da takardu yadda ya kamata. Daga bisani, an dakatar da shari’ar domin warware matsalar. Tun farko, El-Rufai ya bayyana a wata hir...

Obi ba zai iya dawowa ya tsaya takarar shugaban ƙasa ta 2027 a jam’iyyar mu ba – LP

Image
Obi ba zai iya dawowa ya tsaya takarar shugaban ƙasa ta 2027 a jam’iyyar mu ba – LP Shugabar riko ta jam’iyyar Labour Party (LP), Sanata Nenadi Usman, ta bayyana cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a 2023, Peter Obi, ba zai iya dawowa ya tsaya takarar 2027 a ƙarƙashin jam’iyyar ba. Jaridar PUNCH ta rawaito cewa, Usman ta ce dokar zaɓe ta tanadi cewa dole ne jam’iyya ta rufe rajistar mambobinta kwanaki 21 kafin zaɓen fidda gwani, tare da miƙa sunayen ga Hukumar INEC, don haka ba zai yiwu a sake yi wa wani rajista bayan an rufe littafin ba. Ta kuma amince cewa Obi ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasar LP a zaɓen 2023, inda har ya jawo mutane da dama, ciki har da ita kanta, suka bar PDP suka shiga jam’iyyar saboda adalci da daidaito. Usman ta ce dalilin barinta PDP shi ne rashin bai wa yankin kudu tikitin shugaban ƙasa, abin da ta ce bai dace ba. A halin yanzu, jam’iyyar LP na fama da rikicin shugabanci da ya janyo rabuwar kai da sauyin jam’iyya da dama. Kotu ...

Shugaba Tinubu ya ware Naira Biliyan 17 domin walwalar al'umma a mazabu 8,804 na Najeriya

Image
Shugaba Tinubu ya ware Naira Biliyan 17 domin walwalar al'umma a mazabu 8,804 na Najeriya Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da fitar da kudi naira biliyan 17 domin gudanar da wani babban shiri na samar da ci gaba a matakin mazabu (Wards) da ke faɗin ƙasar nan. Wannan tallafi, wanda aka yi wa laƙabi da "Community-Based National Social Action Fund", an kafa shi ne domin taba rayuwar talakawa kai-tsaye a dukkanin mazabu 8,804 na Najeriya, ta hanyar ba su damar gudanar da ayyukan da suka fi damunsu a yankunansu. A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Lafiya da Walwalar Jama’a ta Tarayya ta fitar ranar Laraba, wadda mataimakin daraktan yaɗa labarai, Ado Bako ya sanya wa hannu, an bayyana cewa kowace mazaba za ta haɗa gwiwa ne da ƙungiyoyin sa-kai na cikin gida (CBOs) domin gano ayyukan da suka fi buƙata. Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya bayyana cewa wannan sabon salo ne na mika mulki ga talakawa. Ya ce, "Wannan tsari ya sanya al'umma a gaba waj...

Kotu Ta Ɗage Shari’ar Sarkin Zazzau Saboda Rashin Biyan Tara Da Aka Yiwa Mai Ƙara Wato Alhaji Ibrahim Aminu

Image
Babbar Kotun Jihar Kaduna da ke zamanta a Dogarawa, Zaria, ta yi ƙaramin hukunci a shari’ar batanci da ke tsakanin Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, da tsohon Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim Muhammad Aminu, inda ta hana mai ƙara damar yin jawabi saboda rashin bin umarnin kotu. A zaman da aka ci gaba da shi a ranar Laraba, Mai Shari’a Yakubu Badamasi ya bayyana cewa ba za a bai wa mai ƙara damar yin magana ba, saboda ya gaza bin umarnin kotu da aka riga aka bayar. Kotun ta riga ta ci tarar naira dubu dari biyu (₦200,000) ga mai ƙarar saboda rashin nuna ƙwarewa wajen shigar da ƙarar, tare da la’akari da wahalar da lauyoyin ɓangaren da ake ƙara suka sha wajen zuwa kotu daga Lagos, Abuja da Kaduna. Duk da wannan umarni, mai ƙarar bai biya tarar ba, wanda ya sa kotu ta jingina da ƙa’idar doka da ke cewa wanda ya saɓa wa umarnin kotu ba za a saurare shi ba har sai ya gyara laifinsa. Saboda haka, kotun ta ɗage shari’ar zuwa ranar 16 ga Yuni, 2026, domin a cika sharadin bin u...

Kotu ta umarci a tsare waɗanda ake zargi da shirin juyin mulki a hannun DSS

Image
Kotu ta umarci a tsare waɗanda ake zargi da shirin juyin mulki a hannun DSS Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare wasu mutane shida da ake zargi da hannu a shirin juyin mulki a hannun hukumar tsaro ta farin kaya Kaya (DSS), bayan an gurfanar da su kan tuhume-tuhume guda 13 da suka shafi zargin ta’addanci. A zaman kotun da aka fara da misalin ƙarfe 1:46 na rana a ranar Laraba, Babban Lauyan tarayya, Lateef Fagbemi (SAN), ya shaida wa kotun cewa an shirya tuhumar, inda ya nemi a karanta wa waɗanda ake zargin laifukan da ake tuhumarsu da su. Sai dai shari’ar ta ɗan tsaya na ɗan lokaci bayan wanda ake tuhuma na uku ya bayyana cewa lauyansa ba ya nan saboda rashin lafiya, yayin da lauyan wanda ake tuhuma na shida ya ce wanda yake karewa na fahimtar harshen Larabci da Hausa kaɗai, lamarin da ya sa kotu ta dakatar da zaman domin samar da mai fassara. Da aka koma zaman kotun da misalin ƙarfe 2:18 na rana, dukkanin waɗanda ake tuhumar sun ki amsa laifukansu inda...

Zazzau Emir’s Defamation Case: Court Bars Claimant Over Non-Compliance, Adjourns Proceedings

Image
The Kaduna State High Court sitting in Dogarawa, Zaria, has delivered a significant ruling in the ongoing defamation suit involving the Emir of Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli, and a former Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim Muhammad Aminu, barring the claimant from being heard due to non-compliance with a court order. At the resumed sitting on Wednesday, the presiding judge, Justice Yakubu Badamasi, held that the claimant could not be granted the right of audience, having failed to comply with an earlier directive of the court. The court had previously imposed a fine of ₦200,000 on the claimant for lack of diligent prosecution, citing the inconvenience caused to defence counsel who travelled from Lagos, Abuja, and Kaduna. Despite the order, the claimant failed to settle the fine, prompting the court to invoke the legal principle that a party in disobedience of a subsisting court order cannot be heard until such contempt is purged. Consequently, the court adjourned the matter to Jun...

Ɗan takarar Sanatan Kaduna-ta-Arewa a APC , Sha'aban ya janye takarar

Image
Ɗan takarar Sanatan Kaduna-ta-Arewa a APC , Sha'aban ya janye takarar  Hon. Sani Sha’aban,.Danburan Zazzau ya jaddada janye neman takarar Sanatan Kaduna ta Arewa, tare da bayyana goyon bayan duk wanda APC ta tsayar  Cikin wata sanarwa da iyalan sa su.ka fitar, dauke da sanya hannun Alhaji Ahmad Bamalli ta bayyana cewar bisa wasu dalilai bayan shawarwarin da aka tattauna daga ranar Talata 21/4/2026 ya janye takarar sa. "Muna sanar da dukkannin magoya bayan Hon. Sani Sha'aban cewar ya janye daga neman takarar kujerar Sanata a Shiyyar Kaduna ta Arewa wato (zone one), tare da bayyana goyon baya ga duk dan takarar da APC ta tsayar,"  A cikin sanarwar an bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne na janye takarar ne bisa la’akari da muradun iyalansa. Sanarwar ta ce: “Hon. Sha’aban yana nan daram kan wannan matsaya, kuma ba zai nemi wata kujera ta siyasa a jihar ba. Har ila yau, zai cigaba da biyayya ga jam’iyyar APC, kuma a shirye yake ya bayar da gagarumar gudunmaw...

An samu sabon mai ɗauke da cutar corona a Nijeriya.

Image
An samu sabon mai ɗauke da cutar corona a Nijeriya  Gwamnatin jihar Cross River ta tabbatar da bullar cutar COVID-19 ga wani ɗan ƙasar China mai shekaru 53, wanda yanzu haka yana karɓar magani a asibitin koyarwa na jami'ar Calabar. Kwamishinan lafiya na jihar, Henry Egbe Ayuk ne ya tabbatar da hakan kuma ya ce an ɗauki matakan gaggawa domin hana yaduwar cutar, kuma ya tabbatar wa jama’a cewa babu abin tsoro. Ya ce jami'an lafiya sun fara binciken waɗanda suka yi mu’amala da mara lafiyar, tare da sanya ido a kansu, yayin da ake cewa wannan shi ne karo na farko da aka samu irin wannan rahoto a jihar tun 2022. An kuma shawarci jama’a su bi matakan kariya kamar tsafta, amfani da takunkumi, da kai rahoton duk wanda ya nuna alamun cutar.

Kotun ɗaukaka ƙara ta umarci a kawo Sheikh Abduljabbar domin ya kare kansa

Image
Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Kano ta bayar da umarni ga hukumar kula da gidajen gyaran hali ta ƙasa da ta gabatar da Sheikh Abduljabbar Kabara a gaban kotu domin ci gaba da sauraron ƙarar da ya ɗaukaka. Sheikh Abduljabbar, malamin addinin Musulunci, na tsare a gidan yari ne bayan wani hukunci da Ƙaramar Kotun Shari’a ta yanke, inda ta same shi da laifin batanci tare da yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya. A yayin zaman kotun a ranar Litinin, jagoran alkalai, mai shari’a Mohammed Lawal-Shuaibu, ya bayyana cewa tun da wanda ya shigar da ƙarar ya yi hakan da kansa ba tare da lauya ba, dole ne ya bayyana a gaban kotu domin kare kansa da hujjojinsa. Sauran alkalan da suka zauna tare da shi sun haɗa da Mai shari’a Abubakar Mu’azu-Lamido da Mai shari’a Ahmad Ramat-Mohammed. Alkalin ya ce, “Tunda mai ƙara ya shigar da ƙarar da kansa ba tare da wakilcin lauya ba, wajibi ne ya bayyana a gaban kotu da kansa. Haka kuma, kasancewar yana tsare, an umarci hukumar gidan yari da...

Gwamnatin tarayya ta ware sama da Naira Biliyan 1 a kasafin kuɗi don shari'o'in da suka shafi ta'addanci

Image
Gwamnatin tarayya ta ware sama da Naira Biliyan 1 a kasafin kuɗi don shari'o'in da suka shafi ta'addanci  Gwamnatin tarayya ta ware kimanin Naira biliyan 1.37 a kasafin kuɗin shekarar 2026 domin gurfanar da ‘yan ta’addan Boko Haram da sauran masu aikata laifukan ta’addanci, adadin da ya nuna ƙaruwa mai yawa idan aka kwatanta da Naira miliyan 530 da aka ware a shekarar 2025, wanda ya kai kusan kashi 159 cikin ɗari kamar yadda jaridar PUNCH ta rawaito. Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya rattaba hannu kan kasafin kuɗin 2026 na Naira tiriliyan 68.32, inda aka keɓe Naira tiriliyan 5.41 domin harkokin tsaro. Ƙarin kuɗin na nuni da cewa gwamnati na ƙara maida hankali wajen yaƙi da matsalar rashin tsaro da kuma tabbatar da an gurfanar da masu laifi a gaban kotu. Rahotanni sun nuna cewa kuɗin da aka ware domin shari’o’in ta’addanci ya zama wani muhimmin kaso a cikin kuɗaɗen da ma'aikatar shari'a ke kashewa. A nasa ɓangaren, Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, ya ...

Tazkiyah University Holds Maiden Matriculation Ceremony for 2025/2026 Academic Session in Zaria

Image
Tazkiyah University, Zaria, Kaduna State, on 18 April 2026, held its maiden matriculation ceremony for newly admitted students for the 2025/2026 academic session. The ceremony took place at the university’s multipurpose hall at about 10:00 a.m. In his address, the Vice-Chancellor, Faruk Sarkin Fada, highlighted the global recognition of women’s education and noted that the establishment of the university aligns with international efforts to promote girls’ access to safe and quality education. He explained that the university’s vision is to produce globally competitive graduates equipped with knowledge, character, and leadership capacity. He added that the admission policy reflects national integration, as the pioneer cohort includes students from diverse religious and cultural backgrounds, reinforcing peaceful coexistence and unity. In his remarks, the Proprietor and Founder, Ibrahim Ahmad Maqari, described the ceremony as a defining moment and a dream fulfilled. He noted t...

Nigeria’s AI Boom Faces Governance Gaps, Experts Warn

Image
A new assessment of Nigeria’s artificial intelligence (AI) governance framework has revealed significant gaps in regulation, raising concerns over data privacy, national security, and ethical standards as AI adoption accelerates across key sectors. The report, presented at the Federal Ministry of Finance in Abuja on Thursday, identified critical issues including weak regulatory oversight, lack of transparency, accountability gaps, and risks of algorithmic bias. Stakeholders also highlighted the absence of a comprehensive legal framework guiding AI deployment in the country. Speaking to journalists after the presentation, Dr. Umar Yakubu, Executive Director of the Centre for Fiscal Transparency and Public Integrity, said the rapid growth of AI use in sectors such as banking, agriculture, housing, and healthcare has outpaced governance structures. “We are seeing widespread adoption of AI and significant financial investments, but there are serious national security risks and ...

ABUTH Zaria inducts 267 Health Information technicians, technologists

Image
The Ag. Principal of School of Health Information Management, Ahmadu Bello University Teaching Hospital (ABUTH), Zaria, Dr. Zaharadeen Adamu, has said that the oath-taking and induction ceremony is aimed at formally ushering graduates into the health information management profession and preparing them for the ethical responsibilities ahead. Dr. Adamu stated this on Wednesday during the 2nd oath-taking and induction ceremony of registered Health Information Management Technicians and Technologists held at Ahmadu Bello University, Zaria. He said the ceremony was designed to instill discipline, professionalism and a strong sense of responsibility among the inductees as they begin their careers. He congratulated the 267 graduating students and urged them to be worthy ambassadors of the institution, stressing the need for integrity, dedication and continuous learning in the discharge of their duties. The Head of School also explained that obtaining a professional li...

The Academic Seal: A Moral Critique of Political Endorsement

Image
There is a reason why the PhD is titled "Doctor of Philosophy." Philosophy is a discipline of rigor and gravity. Among its many virtues, it is meant to compel one to think, act, and write with the clarity of a philosopher. But what does it take to truly embody that pattern? It requires a commitment to intellectual integrity that borders on the sacred. Regardless of which philosophical school one leans toward, the minimum expectation is that objectivity, rationality, and a commitment to truth be adequately reflected in one's public discourse. This premise is prompted by an article written by one Professor Shehu A. Goni, which serves as an overt promotion of Mr. Bala Wunti for the governorship of Bauchi State. Every citizen, professor or not, has the right to support any candidate. However, I wish the author had simply signed his name without appending his professorship. Had he done so, no serious observer would have felt the need to respond; it would have been ...

Darajar Ilimi: Tsokaci kan rawar malamai a siyasa

Image
Akwai dalili da yasa ake kiran PhD da “Doctor of Philosophy.” Falsafa fanni ne mai nauyi da zurfi. Daya daga cikin muhimman darajojinta shi ne tana tilasta mutum yin tunani, aiki da rubutu da tsari irin na masanin falsafa. Amma me ake bukata domin kaiwa wannan matsayi? Yana bukatar tsayawa kan gaskiyar ilimi da aminci wanda ya kai matsayin tsarki. Duk wata makarantar falsafa da mutum ya jingina da ita, dole ne a nuna gaskiya, hankali da rikon gaskiya a duk abin da ake rubutawa a bainar jama’a. Wannan tunani ya samo asali ne daga wani rubutu da wani Farfesa, Shehu A. Goni, ya yi, wanda a fili yake nuna goyon baya ga Bala Wunti a matsayin ɗan takarar gwamnan Bauchi. Kowane ɗan ƙasa, ko Farfesa ko ba haka ba, yana da ‘yancin goyon bayan wanda yake so. Amma da ya fi kyau da marubucin ya sanya sunansa kawai ba tare da haɗa da mukaminsa na Farfesa ba. Da hakan ne, da ba za a ɗauki rubutun da muhimmanci ba; za a ɗauke shi a matsayin tallatawa kawai. Amma idan Farfesa ya rubuta lab...

Garo Emerges Front-Runner for Kano Deputy Governorship, Secures Broad APC Bloc Backing

Image
Former Commissioner for Local Government, Hon. Murtala Sule Garo, has emerged as the leading contender for the vacant position of Deputy Governor of Kano State, following what insiders describe as overwhelming support from the “old bloc” of the All Progressives Congress (APC). Sources privy to a high-level stakeholders’ meeting convened by Governor Abba Kabir Yusuf indicate that Garo secured approximately 90 per cent endorsement from party leaders and influential figures present at the gathering. The meeting, according to those familiar with its proceedings, was part of ongoing efforts to consolidate party unity and strengthen governance structures in the state. The development comes in the wake of the resignation of former Deputy Governor, Abdussalam Aminu Gwarzo, which created a vacancy the administration is now seeking to fill through consultations within key political blocs. At the meeting, the governor formally requested the APC’s old bloc to nominate three credible in...

Gyaran layin wutar lantarki: Jihohi 7 za su fuskanci rashin wuta na tsawon makonni 6

Image
Kamfanin Kula da Wuyar Lantarki mai zaman kansa na ƙasa (NISO) ya sanar da cewa jihohi bakwai za su fuskanci ƙarancin wutar lantarki na tsawon makonni shida sakamakon wani shirin gyara da aka tsara a layin wutar Jos–Gombe mai ƙarfin 330kV. A wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Alhamis, kamfanin ya ce za a fara aikin daga ranar 9 ga Afrilu zuwa 22 ga Mayu, 2026. NISO ya bayyana cewa za a riƙa samun katsewar wutar ne duk mako daga ranar Alhamis zuwa Lahadi, tsakanin ƙarfe 9:00 na safe zuwa 6:00 na yamma, domin baiwa aikin girka wayar sadarwa ta fibre optic damar gudana a kan layin. Jihohin da abin zai shafa sun haɗa da Plateau, Gombe, Bauchi, Borno, Adamawa, Taraba da Yobe. Kamfanin ya ce wannan gyara na daga cikin ƙoƙarin sabunta tsarin lantarki na ƙasa domin inganta aiki ta hanyar amfani da sabbin fasahohi kamar tsarin SCADA, tsarin sarrafa makamashi, da kuma ingantaccen sadarwa.

NBTE's Visit To Arewa Ambassadors Int' College Of Health Science And Technology Is A Landmark Recognition -- Council Chairman

Image
BY SANI ALIYU, Zaria  The Chairman Governing Council of Arewa Ambassadors International College of Health Science and Technology, Zaria Alhaji AbdulAziz Suleiman has described the National Board for Technical Education (NBTE) committee visit to the College as a landmark recognitions of the contribution made by the college in producing manpower to the health sector in the country.  AbdulAziz Suleiman who stated this during on the NBTE committee members visit the College for assessment of the programmes run by the College in preparation for their accreditation by the Board.  He said they will ensure that the College received all the necessary support needs to make it more effective and reliable that can be one of the best health institution in the country. The Governing Council Chairman who expressed the College appreciation over what he described as progress the College is attaining Earlier in his welcome address the Collage Provost Malam Murtala Iliyasu said...

Ganduje bashi da ikon bani umarni a APC saboda nine jagoran jam'iyyar a Kano - Abba Gida-Gida

Image
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ba zai iya ba shi umarni ba, yana mai cewa shi ne jagoran jam’iyyar a jihar. Yusuf ya yi wannan bayani ne yayin da yake mayar da martani kan sukar da ake yi masa biyo bayan sauya shekarsa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC, inda ya jaddada cewa bai yi wa tafiyar Kwankwasiyya butulci ba. Da yake jawabi a wani taro da ya yi da mawallafa waƙoƙin sa a jiya a Kano, gwamna Abba ya kara da cewa sauya shekarsa ta samo asali ne sakamakon rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar NNPP. Gwamnan ya kuma ce duk da girmamawar da yake yi wa Ganduje, ba zai amince ya riƙa juya shi ba. A cewar gomna Yusuf “Abin da ke tsakaninmu ni da Ganduje girmama juna ne. Amma ba shi da ikon ba ni umarni, domin ni ne jagora,”

Kotu ta yanke wa wani mutum ɗaurin rai-da-rai bisa yi wa ƴar shekara 9 fyaɗe a Jigawa

Image
Kotu ta yanke wa wani mutum mai suna Bashir A. Umar hukuncin ɗaurin rai-da-rai bayan an kama shi da laifin yi wa yarinya ƴar shekara 9 fyaɗe har ya raunata ta a Jihar Jigawa. Tun a bara kotu ta samu Umar da laifin, sannan ta yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai kan laifin fyade, da kuma ɗaurin shekaru 7 kan laifin jikkata yarinyar. Haka kuma, kotun ta umarce shi ya biya diyyar naira miliyan 1 ga yarinyar. Gwamnatin jihar ta yaba da hukuncin, tana cewa adalci ya tabbata.  Gwamnatin ta kuma kula da lafiyar yarinyar tare da taimaka wa iyayen ta da kyautar gida.

EFCC ta kama wata ƴar Tiktok a Borno kan zargin wulakanta Naira

Image
Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annati ta EFCC ta kama wata mata mai suna Fatima Mohammed a Maiduguri, jihar Borno, bisa zargin wulakanta kudin Najeriya. A cewar hukumar, an kama matar ne bayan wani bidiyo da ya yadu a TikTok inda aka gan ta na goge majina da takardar kudi N500. Jami’an EFCC sun ce sun gano ta tare da cafke ta a cikin garin Maiduguri. Yanzu haka ana tsare da ita yayin da ake ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da ita a kotu bayan kammala binciken. Hukumar ta ce laifin ya sabawa dokar Babban Bankin Najeriya (CBN), wadda ta haramta lalata ko amfani da kudin kasa ta hanyoyin da ba su dace ba, tare da tanadin hukuncin tara ko dauri. Lamarin ya biyo bayan irin wannan hukunci da aka yanke wa wata jarumar Kannywood kwanan nan kan makamancin laifi.

Kotu ta bada belin mutanen da su ka ci zarafin Farfesa Umar Sani Fagge

Image
Kotun majistare mai lamba 53 da ke zamanta a Norman’s Land a Kano ta bada belin wasu mutane uku da ake zargi da cin zarafin Sheikh Farfesa Umar Sani Fagge. Manema labarai sun rawaito cewa, an gurfanar da Adamu Adamu da Salihu Bala da Hassan Umar a gaban alƙalin kotun, Mustapha Sa’ad Datti bisa tuhume-tuhume da su ka hada da hadin baki domin aikata laifi da cin zarafi da kuma tada tarzoma. A yayin zaman kotun a yau Alhamis, alƙalin ya saurari karar inda wadanda ake zargin su ka musanta tuhume-tuhumen. Daga bisani ne lauyansu ya nemi a bads belin su. Kotun ta amince da bayar da belin kan sharadin naira dubu hamsin ga kowanne daga cikinsu tare da samar da masu tsaya musu biyu, daya darakta daya kuma malamin jami’a. Kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 28 ga Afrilu 2026 domin ci gaba da shari’a. Ana zarginsu da yin kalaman ɓatanci a wani taron siyasa a Kwaciri inda a taron wani Isyaku Mai Fenti ya ce, Akuyar Kwaciri ta fi Malam Umar Sani Fagge, kuma ya wallafa bayanin a sha...

Ƴan majalisar APC na Bauchi sun ziyarci Gwamnan Bauchi a yayin da yake shirin sauya sheƙa

Image
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya karɓi bakuncin wasu ’yan majalisar wakilai na jam’iyyar APC daga jihar a gidansa da ke Abuja, yayin da ake rade-radin shirin ficewarsa daga jam’iyyar PDP kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito. Rahotanni sun ce gwamnan ya gana da ’yan majalisar ne domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan shirin sauya sheƙarsa zuwa jam’iyya mai mulki. Bayan ganawar, ɗan majalisar mai wakiltar mazaɓar Toro, Dabo Ismail, ya bayyana cewa an gayyace su ne domin tattauna sabbin sauye-sauyen siyasa da ke gudana a ƙasar, musamman a jihar Bauchi. Ya ce sun tattauna muhimman batutuwa da suka shafi ci gaban jihar, tare da samun wasu matsaya masu kyau. Ya ƙara da cewa nan gaba kaɗan za su bayyana matsayarsu, yayin da za su ci gaba da tuntuɓar sauran masu ruwa da tsaki tare da sanar da su sakamakon ganawar. A baya, a ranar 1 ga Afrilu, Bala Mohammed ya karɓi shugabannin APC na ƙasa da wasu gwamnoni a Bauchi, ciki har da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Nentawe Yilwa...

Sanata Kabiru Marafa ya fice daga jam’iyyar APC ya faɗa ta ADC

Image
Tsohon Sanatan Zamfara-ta-Tsakiya, Kabiru Marafa, ya sanar da sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar ADC, inda ya zargi jam’iyyar APC da makarkashiya. Sauyin sheƙar tasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da rikici a cikin jam’iyyar ADC, wanda ya kai ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) kin amincewa da shugabannin bangarorin jam’iyyar, bayan hukuncin da Kotun Daukaka Ƙara ta yanke a ranar 12 ga Maris. Jaridar TheCable ta rawaito cewa a cikin wata sanarwa da Mansur Haruna, Darakta-Janar na sabuwar kungiyar yaɗa labaransa ya fitar a yau Alhamis, Marafa ya ce sauyin jam’iyyar da ya yi wani babban mataki ne a tarihin siyasar jihar Zamfara. Ya kuma bayyana cewa magoya bayansa da tsarin siyasar da yake da shi sun biyo shi zuwa sabuwar jam’iyyar. Tsohon dan majalisar dattawan ya ce matakin ya biyo bayan taron manyan masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Kaduna, inda ya tattauna sosai da abokan siyasa da kuma magoya bayansa. Ya ƙara da cewa nan gaba kadan za a gudanar da babban...

PDP da ADC sun yi ganawar sirri a Abuja kan yiwuwar hadaka gabanin zaɓen 2027

Image
Wata babbar tawaga ta jam’iyyar PDP karkashin jagorancin Tanimu Turaki ta gudanar da ganawar sirri da shugabannin jam’iyyar ADC da David Mark ke jagoranta a birnin Abuja kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta rawaito. Rahotanni sun ce tawagar ta PDP ta isa gidan Mark da ke Apo Legislative Quarters da misalin karfe 4:50 na yamma a ranar Laraba. Majiyoyi sun bayyana cewa ganawar na daga cikin tattaunawa da ake yi domin duba yiwuwar kulla kawance tsakanin PDP da ADC gabanin babban zaben shekarar 2027. Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde; tsohon ministan yada labarai kuma jigo a PDP, Jerry Gana; da tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu, tare da mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar (NWC). Haka kuma, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar; dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi; tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso; da tsohon gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal, duk sun halarci taron. Sauran sun h...

Gwamnan Kano ya yi alƙawarin magance matsalar ruwa

Image
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sha alwashin magance matsalar ƙarancin ruwa a jihar, inda ya kai ziyarar duba dukkan matatun ruwa domin tantance halin da suke ciki. A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mustapha Muhammad, ya fitar, ya ce ziyarar na da nufin gano matsalolin da ke hana samar da wadataccen ruwa a wasu sassan jihar da kuma nemo hanyoyin warware su. Gwamnan ya fara ziyarar ne daga matatar ruwan Tamburawa, inda ya duba muhimman kayan aiki da bututun rarraba ruwa.  An gano matsaloli da suka haɗa da zubewar ruwa daga bututu, lalacewar injuna da kuma tsofaffin kayan aiki. Ya jaddada kudirin gwamnatinsa na gyara dukkan sassan da suka lalace domin inganta samar da ruwa ga al’umma. Haka kuma, gwamnan ya bayyana cewa za su haɗa kai da kamfanin kasar Sin na CGC domin samar da mafita mai dorewa ga matsalar ruwa a jihar. Ya ƙara da cewa samar da tsaftataccen ruwan sha mai inganci na daga cikin manyan manufofin gwamnatinsa, yana mai tabbatar da cewa za a yi ...

Yusuf Buhari ya baiyana buƙatar da ta tsayawa takarar dan majalisar wakilai

Image
  Ɗan marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, wato Yusuf Buhari, ya baiyana aniyarsa ta tsayawa takara a zaɓen 2027. Manema labarai sun rawaito cewa Yusuf na son yin takarar kujerar Majalisar Wakilai da yankin Sandamu/Daura/Mai’Adua a jihar Katsina, ƙarƙashin jam’iyyar APC. Wani tsohon mai taimaka wa shugaban ƙasa kan yaɗa labarai, Bashir Ahmad, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X, inda ya ce Yusuf ya ɗauki wannan mataki ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki na yankin na su. 

Babu hannun Tinubu a rikicin ADC, in ji Onanuga

Image
Mai magana da yawun Shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba shi da hannu a rikicin cikin gida da ke addabar ADC, yana mai cewa matsalolin da jam’iyyar ke fuskanta “su suka jawo wa kansu.” Onanuga ya yi wannan bayani ne yayin da yake mayar da martani kan zarge-zargen da ake yi cewa akwai sa hannun gwamnatin tarayya a rikicin jam’iyyar. Ya kuma soki tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, inda ya ce ya bar jam’iyyarsa cikin rikici ba tare da warware matsalolinta ba. A cewarsa, Obi bai nuna ƙwarewa wajen gina jam’iyya mai ƙarfi ko ingantaccen tsari ba. Haka zalika, Onanuga ya zargi tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da hannu wajen sayen jam’iyyar ADC, yana mai cewa wannan mataki ne ya haifar da rikice-rikicen da jam’iyyar ke fama da su a halin yanzu. A ƙarshe, ya ce tasirin siyasar Peter Obi a zaɓen 2027 zai dogara ne kacokan kan samun tikitin tsayawa takara, yana mai ƙara da cewa nasarar da ...