DSS ta saki Walida wacce ake zargin an sace ta, an sauya mata addini a Jigawa
Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta saki Walida Abdulhadi Ibrahim, yarinyar da aka sace daga jihar Jigawa , tare da miƙa ta ga Gwamna Umar Namadi a hedikwatar hukumar da ke Abuja.
Gwamnan ya ce za a ci gaba da riƙe Walida a kulawar gwamnatin jihar har sai kotu ta warware dukkan muhawarar da ke tattare da zargin sace ta, sauya addini da kuma batun kulawa da ita.
Ya tabbatar da cewa za a ba ta cikakken tsaro tare da kula da lafiyarta, inda ya ƙara da cewa jaririyar da ta haifa ma za ta kasance a kulawar gwamnati.
Babban Daraktan DSS, Adeola Oluwatosin Ajayi, ya ce tsare ta da aka yi tun Janairu ya kasance ne domin bin doka da kuma kare lafiyarta yayin da ake bincike.
Ya ce duk da miƙa ta ga gwamnatin Jigawa, DSS da sauran hukumomi za su ci gaba da sa ido kan lamarin.
An dai sace Walida ne tun 2023 daga Hadejia, sannan daga baya ta tsinci kanta a Abuja tare da wani jami’in DSS mai suna Ifeanyi Onyewuenyi, wanda ke ci gaba da tsare a hannun hukumar domin bincike.
Comments
Post a Comment