EFCC ta sake gurfanar da Malami, matarsa da ɗansa kan zargin “badakalar kuɗi”
Hukumar yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta sake gurfanar da tsohon Antoni Janar na ƙasa (AGF), Abubakar Malami, tare da matarsa, Asabe Bashir, da ɗansa, Abdulaziz, bisa zargin aikata laifin badakalar kuɗi.
An sake gurfanar da waɗanda ake tuhuma a ranar Juma’a a gaban Joyce Abdulmalik, alkaliyar babbar kotun tarayya da ke Abuja, bayan da aka sauya alƙalin da ke sauraron shari’ar.
A zaman da aka koma ci gaba da shari’ar, lauyan hukumar EFCC, Jibrin Okutepa, ya shaida wa kotu cewa shari’ar na zuwa ne karo na farko a gaban sabuwar alkaliyar da aka ba ta, sannan ya roƙi kotu da ta karɓi amsar tuhumar daga bakin waɗanda ake zargi.
Comments
Post a Comment