Ficewar Fintiri daga PDP zuwa APC, illace babba ga Atiku a jihar Adamawa
Mai bai wa Shugaba Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai Bayo Onanuga, ya bayyana sauyin sheƙar Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, zuwa jam’iyyar APC a matsayin babban sauyi na siyasa da zai bai wa jam’iyyar rinjaye a jihar.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Juma’a, Onanuga ya ce matakin da Fintiri ya ɗauka na ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa APC zai ƙara wa jam’iyyar da ke mulki ƙarfi a Adamawa, yana mai cewa wannan lamari babbar illa ce ga Atiku Abubakar.
Ya bayyana cewa sauyin ya shafi makomar siyasar jihar gaba ɗaya, musamman yayin da zaɓen shugaban ƙasa ke ƙaratowa.
Comments
Post a Comment