INEC ta mayar da lokacin zaɓen 2027 kafin Azumi
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta sanya ranar 16 ga Janairu, 2027, a matsayin sabuwar ranar gudanar da zaɓen Shugaban Ƙasa da na ‘yan Majalisar Tarayya.
Haka kuma, hukumar ta ayyana ranar 6 ga Fabrairu, 2027, a matsayin sabuwar ranar gudanar da zaɓen gwamnonin jihohi da na ‘yan Majalisun Dokokin Jihohi.
A sanarwar da hukumar ta fitar ta bayyana cewa za a gudanar da zaɓen fidda gwani na jam'iyyun daga watan Afrilu zuwa Mayu na 2026
Comments
Post a Comment