Jam’iyyun siyasa na fuskantar yiwuwar hana su shiga zaɓen 2027 kan rajistar mambobi ta yanar gizo
Jam’iyyun siyasa na iya rasa damar tsayar da ’yan takara a zaɓen 2027 idan ba su bi sashe na 77 na dokar zaɓe ta 2026 ba kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.
A ranar 18 ga Fabrairu, Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu kan dokar gyaran zaɓe bayan majalisar tarayya ta amince da ita.
Sashen na 77(2) ya tanadi cewa dole jam’iyyun siyasa su miƙa cikakkiyar rajistar mambobinsu ta yanar gizo ga INEC aƙalla kwanaki 21 kafin gudanar da zaɓen fidda gwani.
Rajistar dole ta ƙunshi sunaye, jinsi, ranar haihuwa, adireshi, jiha, ƙaramar hukuma, gunduma, rumfar zaɓe, lambar shaidar ɗan ƙasa (NIN) da hoto, a takarda da kuma a na’ura.
Sashen na 77(7) ya ce duk jam’iyyar da ta gaza miƙa rajistar cikin wa’adin da aka kayyade ba za ta samu damar tsayar da ɗan takara ba.
INEC ta fitar da sabon jadawalin zaɓe, inda ta sanya 16 ga Janairu, 2027, a matsayin ranar zaɓen shugaban ƙasa da na majalisar tarayya, sai 6 ga Fabrairu, 2027, don zaɓen gwamnoni da majalisun jihohi. Ta kuma umarci jam’iyyu su miƙa rajistarsu kafin 21 ga Afrilu, tare da gudanar da zaɓen fidda gwani tsakanin 23 ga Afrilu da 30 ga Mayu.
Jam’iyyun adawa, ciki har da ADC, sun yi watsi da tanadin, suna zargin cewa an tsara shi ne domin tauye dimokuraɗiyya.
Kakakin ADC, Bolaji Abdullahi, ya ce sashen wani “shinge ne da aka gina da gangan” domin fitar da jam’iyyun adawa daga tsarin zaɓe.
Shi ma Ose Anenih ya ce jam’iyyun adawa na fuskantar ƙalubale wajen cika sharuddan, yana mai hasashen cewa akwai yiwuwar jam’iyya ɗaya ko biyu kacal su iya tsayar da ’yan takara a 2027.
Comments
Post a Comment