John Oyegun: Shugabannin ADC na Kudu maso Kudu sun amince da takarar Amaechi a 2027
John Odigie-Oyegun, tsohon gwamnan Edo, ya ce shugabannin ADC na yankin Kudu maso Kudu sun amince da kudirin takarar shugaban kasa na Rotimi Amaechi, tsohon ministan sufuri kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.
Oyegun ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin taron tuntuba na shugabannin ADC na Kudu maso Kudu da aka gudanar a Benin City, babban birnin jihar Edo.
Ya ce Amaechi ya sanar da shugabannin yankin Kudu maso Kudu aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa.
“Mun yi farin ciki cewa ɗanmu, Rotimi Amaechi, ya yi amfani da wannan taro wajen sanar da mu a hukumance aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa ta wannan babbar ƙasa tamu,” in ji Odigie-Oyegun.
“Zan iya sanar da ku cewa an cimma matsaya baki ɗaya domin ba shi dukkan goyon bayan da yake buƙata wajen cimma burinsa.”
A watan Yuli na shekarar 2025, Amaechi ya ce zai amince ya yi wa’adi guda ɗaya kacal idan ya samu tikitin takarar ADC kuma ya lashe zaɓen shugaban kasa na 2027.
A farkon wannan wata, tsohon ministan ya roƙi ADC da ta yi la’akari da ɗan takara daga Kudu a matsayin dan takarar shugaban kasa gabanin zaɓen 2027.
“Zan goyi bayan duk wanda ya fito. Amma ina kuma ba ADC shawara ta duba ta zaɓi mafi dacewa wanda zai iya gamsar da ’yan Najeriya cewa za a gyara al’amura,” in ji Amaechi.
Comments
Post a Comment