Akwai yiyuwar mutum 2 sun rasa rayukansu a rikicin kabilanci a jihar Adamawa

Rahotanni daga jihar Adamawa na cewa mutum biyu sun rasa rayukansu a sabon rikicin da ya tashi tsakanin al’ummomin Chobo da Bachaman a karamar hukumar Lamurde, ta jihar.

Mai magana da yawun ‘yan sanda na jihar, Suleiman Yahaya-Nguroje, ya ce rikicin ya barke ne a daren Asabar bayan wasu matasan Chobo sun farmaki garin Lamurde, inda suka yi harbi, abin da ya sa matasan Bachaman suka yi ramuwar gayya.

An ruwaito cewa an tura jami’an ‘yan sanda domin dawo da zaman lafiya, yayin da ake ci gaba da tattara rahotannin hasarar rayuka.

Wannan rikici wanda ya samo asali ne a kan rikicin kasa a yankin, wanda a cikin watanni shida da suka gabata ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 30, musamman mata.

Comments

Popular posts from this blog

Zazzau Emir’s Defamation Case: Court Bars Claimant Over Non-Compliance, Adjourns Proceedings

Alleged 419 Case: Senator Abdu Kwari in Fresh Court Battle Over Property Deal

Maradin, Dan Saran and Wakilin Watsa Labaran Zazzau Honour Loyal Aides with Traditional Titles