An karrama Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da lambar yabo ta “Gwamnan Shekara ta 2025”

An karrama Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da lambar yabo ta “Gwamnan Shekara ta 2025”daga Silverbird Group, a wani taro da aka gudanar a Eko Hotels and Suites, Victoria Island, a ranar Lahadi.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar manema labarai da Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan Kano, Mustapha Muhammad, ya fitar.

A cewar masu shirya taron, an ba gwamnan wannan lambar yabo ne sakamakon irin kokarinsa wajen tabbatar da shugabanci nagari da kuma aiwatar da manufofi da ayyukan raya kasa da suka shafi rayuwar al’umma kai tsaye.

Sanarwar ta ce tun bayan fara wannan gwamnati, an samu sauye-sauye a fannoni daban-daban da suka hada da ilimi, kiwon lafiya, gine-gine da ababen more rayuwa, da kuma bunkasa harkar noma.

Masu shirya taron sun kuma bayyana gwamnan a matsayin jagora mai hangen nesa wanda ke kokarin daukaka martabar jihar Kano, tare da jaddada cewa shirin “Kano First Agenda” ya kara karfafa tafiyar ci gaban jihar.

Sai dai gwamnan bai samu damar halartar taron ba sakamakon wasu uzurori. Mai ba shi shawara kan harkokin cikin gida, Alhaji Bala Usman, ne ya wakilce shi tare da karbar lambar yabon a madadinsa.

A sakon da aka gabatar a madadinsa, gwamnan ya gode wa Silverbird Group bisa wannan karramawa, tare da taya sauran wadanda aka karrama murna. Ya kuma bukace su da su dauki wannan lambar yabon a matsayin kwarin gwiwa na kara himma wajen hidimtawa al’umma.

An bayyana cewa wannan karramawa na daga cikin lambobin yabo da gwamnan ke samu daga kungiyoyi daban-daban, bisa ayyukan raya kasa da gwamnatin sa ke aiwatarwa a jihar Kano.

Comments

Popular posts from this blog

Zazzau Emir’s Defamation Case: Court Bars Claimant Over Non-Compliance, Adjourns Proceedings

Alleged 419 Case: Senator Abdu Kwari in Fresh Court Battle Over Property Deal

Maradin, Dan Saran and Wakilin Watsa Labaran Zazzau Honour Loyal Aides with Traditional Titles