Ayyukan tituna a Kaduna za su taimaka wajen samun nasarar Uba Sani a 2027 - KADRA


Manajan darakta na hukumar kula da tituna ta Jihar Kaduna (KADRA), Dakta Abdullahi Baba-Ahmed, ya ce manyan ayyukan tituna da ake yi a fadin jihar za su ƙara wa Gwamna Uba Sani ƙarfi wajen samun nasara a zaɓen 2027.

Ya bayyana haka ne yayin da yake karɓar wata ƙungiyar matasa, inda ya ce gwamnatin Sani ta aiwatar da sama da ayyukan tituna 140, masu tsawon kusan kilomita 1,335 cikin shekaru uku, wanda ya ce ba a taɓa irin sa ba a Arewa.

A cewarsa, fiye da kashi 60 cikin 100 na ayyukan sun kammala, yayin da ake sa ran kammala sauran kafin ƙarshen wa’adin farko na gwamnati.

Baba-Ahmed ya ce ayyukan sun shafi dukkan yankunan jihar, har da karkara da wasu al’umma ke ganin irin waɗannan ayyuka a karon farko cikin shekaru da dama.

Ya ƙara da cewa titunan sun taimaka wajen sauƙaƙa zirga-zirga, bunƙasa kasuwanci da kuma haɗa al’umma.

Daga cikin manyan ayyukan akwai titin Gadar Gayan–Kujama mai tsawon kilomita 35 da gada a kan kogin Kaduna, wanda ya ratsa ƙauyuka 76.

Ya bayyana cewa irin wannan ci gaba ya sa jama’a ke nuna goyon baya ga gwamnatin, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen sake zaɓen Gwamna Sani a 2027.

Shi ma mai magana da yawun ƙungiyar matasan, Abdullahi Umar, ya yaba da inganci da saurin kammala ayyukan, yana mai cewa hakan na ƙara tabbatar da nasarar gwamnati a zaɓe mai zuwa.

Comments