Da yiwuwar farashin gangar mai ya kai $150 nan da kwanaki uku — Ministan makamashi na Qatar
Ministan makamashi na ƙasar Qatar, Saad Al‑Kaabi, ya yi gargadin cewa farashin ɗanyen mai na duniya na iya kaiwa dala 150 a kowace ganga cikin makonni biyu zuwa uku idan jiragen dakon mai suka ci gaba da kasa wucewa ta mashigin ruwa na Strait of Hormuz.
Al-Kaabi ya bayyana haka ne a wata hira da jaridar Financial Times, inda ya ce rikicin da ake yi tsakanin Iran da ƙawayen Amurka da Israel ya haifar da barazanar tsaro a yankin, lamarin da ya sa wasu manyan kamfanonin jigilar kaya suka dakatar da zirga-zirga ta mashigin Hormuz da kuma Suez Canal.
Ya ce idan wannan matsala ta ci gaba, kasuwar makamashi ta duniya za ta fuskanci matsananciyar tangarda, inda kuma farashin iskar gas zai iya tashi har zuwa dala 40 a kowace MMBtu.
Ministan ya kuma ce kamfanonin mai na yankin Tekun Fasha na iya ayyana force majeure, wanda zai sa su dakatar da fitar da makamashi zuwa kasuwannin duniya.
A wani bangare kuma, kamfanin makamashi na gwamnati QatarEnergy ya dakatar da samar da iskar gas mai ruwa (LNG) bayan hare-haren sojin Iran kan wasu cibiyoyinsa.
Haka kuma kamfanin Saudi Aramco ya rufe matatar mai ta Ras Tanura oil refinery bayan wata gobara da ta tashi sakamakon hari da jirgin mara matuki na Iran.
Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya riga ya fara shafar farashin man fetur a Nigeria, inda kamfanin NNCPL ya kara farashin lita zuwa naira 933 a Lagos da kuma naira 960 a Abuja.
Comments
Post a Comment