Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Tambuwal/Kebbe a jihar Sokoto, Abdussamad Dasuki ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP, inda ya koma ADC


Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Tambuwal/Kebbe a jihar Sokoto, Abdussamad Dasuki ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP, inda ya koma ADC.

A cikin wasiƙar da ya aika wa shugaban PDP na mazabar Dogon Daji/Salah Ward a ƙaramar hukumar Tambuwal, mai ɗauke da kwanan wata 15 ga Maris, 2026, Dasuki ya ce rikicin shugabanci da ya daɗe yana addabar jam’iyyar ne ya sa ya yanke shawarar barin jam’iyyar.


Ya bayyana cewa matsalolin cikin gida na jam’iyyar sun raunana ƙarfin PDP wajen taka rawar da ta kamata a matsayin babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya.

Dan majalisar ya ce ya ɗauki matakin ne bayan tattaunawa da abokan siyasarsa da kuma al’ummar mazabarsa, inda suka nuna damuwa kan halin da jam’iyyar da kuma ƙasar ke ciki.

Comments

Popular posts from this blog

Zazzau Emir’s Defamation Case: Court Bars Claimant Over Non-Compliance, Adjourns Proceedings

Alleged 419 Case: Senator Abdu Kwari in Fresh Court Battle Over Property Deal

Maradin, Dan Saran and Wakilin Watsa Labaran Zazzau Honour Loyal Aides with Traditional Titles