Dangote ya rage farashin man fetur


Matatar man Dangote ta sanar da rage farashin man fetur daga naira 1,175 kan kowace lita zuwa naira 1,075 wato ragin naira 100 kenan.

Wata sanarwa da matatar ta fitar a shafinta na X ta bayyana cewa matakin ya biyo bayan saukar farashin danyen mai a kasuwannin duniya kuma anyi hakan ne bisa tsarin sabon farashi da kamfanin ya fitar.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa matatar ta rage farashin man dizal zuwa naira 1,430 kan kowace lita daga tsohon farashin naira 1,620.

Matatar ta jaddada ƙudurinta na taimakawa wajen karfafa tsaron makamashi a Najeriya tare da la’akari da halin tattalin arzikin da ‘yan kasar ke ciki in ji babban jami'in.

Wannan shi ne karo na farko da aka rage farashin bayan ƙarin sau uku a jere da aka yi a makonnin baya wanda ya sa farashin man ya yi matukar tashi.

Comments

Popular posts from this blog

Zazzau Emir’s Defamation Case: Court Bars Claimant Over Non-Compliance, Adjourns Proceedings

Alleged 419 Case: Senator Abdu Kwari in Fresh Court Battle Over Property Deal

Maradin, Dan Saran and Wakilin Watsa Labaran Zazzau Honour Loyal Aides with Traditional Titles