Gwamna Abba Gida Gida ya ƙaddamar da rabon buhunan shinkafa 100,000 na gidauniyar Dangote
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da rabon buhunan shinkafa 100,000 da gidauniyar Aliko Dangote ta bayar domin tallafa wa marasa karfi a jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Mustapha Muhammad, ya fitar a Kano, gwamnan ya gode wa gidauniyar bisa wannan tallafi, yana mai cewa ya zo a daidai lokaci musamman a watan Ramadan.
Yusuf ya tabbatar da cewa za a raba tallafin cikin gaskiya da adalci ta hanyar shugabannin al’umma da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa ya kai ga waɗanda aka nufa da shi.
Shi ma kwamishinan noma da albarkatun ƙasa na jihar, Dakta Danjuma Mahmud, ya yaba wa gidauniyar Dangote kan ba gwamnatin jihar damar kula da rabon tallafin kai tsaye.
Comments
Post a Comment