Gwamna Abba ya rushe ma’aikatar ilimi mai zurfi yayin da mataimakin Gwamna ya rasa mukamin sa na kwamishina
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da rushe Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi ta jihar, matakin da ya sa Mataimakin Gwamnan jihar, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya daina rike mukamin kwamishinan da ke kula da ma’aikatar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Lahadi.
Sanarwar ta ce gwamnatin jihar ta hade Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi da Ma’aikatar Ilimi domin karfafa daidaiton gudanarwa tare da hanzarta aiwatar da gyare-gyare a bangaren ilimi a jihar.
A karkashin sabon tsarin, ma’aikatar da aka hade za ta ci gaba da aiki ne a karkashin suna Ma’aikatar Ilimi. Haka kuma za a kafa wani sashe na musamman mai kula da Ilimi Mai Zurfi a cikin ma’aikatar domin kula da harkokin manyan makarantu.
Sanarwar ta kara da cewa wannan sashe zai kasance karkashin jagorancin Babban Sakatare tare da samun goyon bayan ma’aikatan da suka dace domin tabbatar da ingantaccen gudanar da cibiyoyin ilimi mai zurfi a jihar.
Har ila yau, dukkan hukumomi da ke karkashin tsohuwar Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi, ciki har da Hukumar Bada Tallafin Karatu (Scholarship Board), za su koma karkashin Ma’aikatar Ilimi. Haka kuma jami’o’in da gwamnatin jihar ta mallaka da sauran cibiyoyin ilimi mai zurfi za su kasance karkashin kulawar sabon sashen da aka kafa.
Gwamnatin ta bayyana cewa wannan mataki na daga cikin gyaran da take yi a bangaren ilimi domin sake farfado da shi, kawar da maimaita ayyuka tsakanin ma’aikatu, inganta hadin kai wajen tsara manufofi a dukkan matakan ilimi tare da rage kudin tafiyar da gwamnati.
Gwamna Yusuf ya ce gyaran tsarin na da nufin rage kashe kudaden gwamnati tare da kara inganci, gaskiya da rikon amana a tafiyar da harkokin ilimi a Jihar Kano.
Ya kuma jaddada kudurin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da manyan gyare-gyare da za su farfado da bangaren ilimi tare da tabbatar da kyakkyawar makoma ga matasan jihar.
A karshe, gwamnan ya umurci Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar da na Shugaban Ma’aikatan Jihar da su tabbatar da aiwatar da sauye-sauyen cikin gaggawa tare da daidaita ayyukan ma’aikatun da abin ya shafa domin samun sauyin cikin sauki.
Comments
Post a Comment