Gwamna Dauda Lawal ya zamanantar da tsarin tattara kuɗin shiga a Zamfara daga biyan kuɗi hannu zuwa ta intanet
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da karɓar duk wani kuɗin shiga na gwamnati ta hanyar tsabar kuɗi a faɗin jihar, domin ƙarfafa tsarin dijital, daidaita bayanan ma’aikatu da hukumomi, ba da damar sa ido kai tsaye, da kuma rage asarar kuɗaɗen shiga.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wani taron wayar da kai kan Dokokin Gyaran Haraji na Nijeriya 2025, wanda Hukumar Tara Haraji ta Jihar Zamfara ta shirya a Gusau.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, gwamnan ya bayyana cewa burin jihar na tara kuɗaɗen shiga na cikin gida (IGR) na shekarar 2026 tsakanin naira biliyan 38 zuwa 42 ya ta’allaka ne kan sabbin gyare-gyaren da aka fara aiwatarwa da kuma faɗaɗa tsarin bin doka.
Comments
Post a Comment