Gwamna Radda ya bada zakkar Naira miliyan 50 daga dukiyar sa zuwa hukumar Zakka da Waƙafi ta Jihar Katsina


Gwamnan Jihar Katsina, Dr. Dikko Umaru Radda PhD. ya Kaddamar da bada Naira miliyan 50 na wani sashe daga cikin zakkarsa, wanda ya baiwa Hukumar Zakka da Waqafi ta Jihar Katsina.

Yayin da ya ke kaddamarwa ya bayyana cewa tunda ya fara fitar da zakka dukiyarsa ke karuwa.

Ya kuma bayyana irin alkairan da fitar da Zakka ke kawo ga al'umma wanda hakan ya sanya Gwamnatinsa ta kafa Hukumar Zakka da Waqafi. 

A na shi Jawabin Shugaban Gammayar Kungiyoyin Zakka da Wakafi ta Nigeria, kuma Mataimakin Sakatare na Zakka da Wakafi ta duniya Engr. Muhammad Lawal Maidoki ya bayyana Gwamnan jihar Katsina a matsayin abin koyi wanda yake fitar da hakkin Allah.

A na shi Jawabin Shugaban Hukumar Zakka da Wakafi Dr. Ahmad Musa Abdullahi ya bayyana yadda Mai Girma Gwamna ya ke ba Hukumar cikakken goyon baya tun daga sadda a ka kafa hukumar.

Cikin wanda suka kaddamar da ta su Zakkar akwai Mai Girma Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Mallam Faruk Lawal Jobe (Sarkin Fulani Joben Katsina), Mai Girma Sanata Abdul'aziz Musa Yar'adua, Alhaji Dahiru Usman Sarki (Danmarna).

Comments

Popular posts from this blog

Zazzau Emir’s Defamation Case: Court Bars Claimant Over Non-Compliance, Adjourns Proceedings

Alleged 419 Case: Senator Abdu Kwari in Fresh Court Battle Over Property Deal

Maradin, Dan Saran and Wakilin Watsa Labaran Zazzau Honour Loyal Aides with Traditional Titles