Gwamnatin Jigawa ta sallami ‘yan kwangila 22 kan zargin almundahana a shirin ciyarwar Ramadan



Gwamnatin Jihar Jigawa ta sallami ‘yan kwangila da kamfanoni 22 da ke gudanar da shirin ciyar da jama’a abincin buda baki a watan Ramadan, bayan zargin magudi, rashin ingancin abinci da kuma almundahanar kudade.

Kwamishinan Ma’aikatar Jin Kai da Ayyuka na Musamman ta jihar, Auwalu Sankara, ya bayyana haka a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Dutse ranar Juma’a.

Ya ce an dauki matakin ne bayan rahotannin sa ido da korafe-korafen jama’a da suka nuna cewa wasu daga cikin ‘yan kwangilar na bada abinci mara inganci, rage adadin abinci, da kuma tafiyar da kudaden shirin ba bisa ka’ida ba.

Shirin ciyarwar, wanda gwamnan jihar Umar Namadi ya kaddamar, na da nufin ciyar da mutane kimanin miliyan 7.9 a cibiyoyi 640 a fadin jihar domin tallafawa marasa karfi a watan Ramadan na 2026.

Sankara ya ce gwamnati ba za ta lamunci duk wani aiki da zai bata manufar shirin jin kai na gwamnatin jihar ba, yana mai jaddada cewa an fara daukar sabbin ‘yan kwangila domin maye gurbin wadanda aka kora.

Ya kara da cewa matakin na nuna kudurin gwamnati wajen kare kudaden jama’a da kuma tabbatar da cewa al’ummar Jigawa sun samu ingantaccen tallafi.

Comments

Popular posts from this blog

Zazzau Emir’s Defamation Case: Court Bars Claimant Over Non-Compliance, Adjourns Proceedings

Alleged 419 Case: Senator Abdu Kwari in Fresh Court Battle Over Property Deal

Maradin, Dan Saran and Wakilin Watsa Labaran Zazzau Honour Loyal Aides with Traditional Titles