Gwamnatin jihar Jigawa ta kara alawus din masu unguwanni daga N3,000 zuwa N10,000

Gwamnan Umar Namadi na jihar Jigawa ya amince da ƙara alawus ɗin da ake bai wa masu unguwa na wata-wata daga naira dubu uku zuwa naira dubu goma.

An sanar da wannan mataki ne bayan zaman majalisar zartarwar jiha da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Dutse a ranar Talata.

Da yake yi wa manema labarai bayani kan sakamakon zaman, kwamishinan muhalli da sauyin yanayi na jiha, Dr. Nura Kazaure, ya ce karin alawus ɗin na nuna kulawa da tausayi da gwamnatin gwamnan ke nunawa shugabannin gargajiya na matakin ƙasa.

An dauki matakin ne, duba da halin da tattalin arziki ke ciki da kuma nauyin da shugabannin gargajiya ke ɗauka wajen hidimar al’umma.

Comments

Popular posts from this blog

Zazzau Emir’s Defamation Case: Court Bars Claimant Over Non-Compliance, Adjourns Proceedings

Alleged 419 Case: Senator Abdu Kwari in Fresh Court Battle Over Property Deal

Maradin, Dan Saran and Wakilin Watsa Labaran Zazzau Honour Loyal Aides with Traditional Titles