Hadimin Shugaban Nijeriya, Ja’oji ya ajiye mukaminsa domin tsayawa takara a zaɓen 2027



Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Nijeriya kan harkokin zama ɗan ƙasa da shugabanci, Nasir Bala Aminu, ya ajiye aikinsa gabanin zaɓen 2027.

Matakin na zuwa ne bayan umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu cewa duk masu riƙe da muƙaman siyasa da ke son tsayawa takara su sauka kafin ƙarshen Maris 2026.

Ja’oji ya gode wa shugaban ƙasa bisa damar da aka ba shi, yana mai cewa an naɗa shi ne domin ƙarfafa matasa su taka rawa wajen gina ƙasa.

Rahotanni sun nuna cewa yana shirin tsayawa takarar kujerar majalisar wakilai ta Tarauni, yayin da magoya bayansa ke nuna goyon baya ga burinsa na siyasa.

Comments

Popular posts from this blog

Zazzau Emir’s Defamation Case: Court Bars Claimant Over Non-Compliance, Adjourns Proceedings

Alleged 419 Case: Senator Abdu Kwari in Fresh Court Battle Over Property Deal

Maradin, Dan Saran and Wakilin Watsa Labaran Zazzau Honour Loyal Aides with Traditional Titles