Hisbah ta yi barazanar gurfanar da masu tashe a kotu



Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta yi barazanar kai duk wanda aka kama yana gudanar da tashe zuwa kotu, sakamakon yadda wasu ke amfani da al’adar wajen aikata laifuka da tayar da hankalin jama’a.

A wata sanarwa da Mataimakin Babban Kwamandan hukumar, Dakta Mujahiddin Aminuddin, ya fitar, ya ce wasu bata-gari na amfani da tashe wajen yin sare-sare, doke-doke da cin mutuncin mutane, a wasu lokuta har da firgita al’umma.

Ya tunatar da jama’a cewa watan Ramadan lokaci ne na ibada, istigfari, tuba, rahama da kuma ‘yantar da bayi daga wuta. Ya kara da cewa bai dace a rika amfani da sunan Musulunci ko addini wajen cin mutunci ko cin zarafin wani ba, domin hakan ya sabawa koyarwar addini.

Dakta Aminuddin ya yi kira ga al’umma da su bi doka tare da guje wa duk wani abu da zai iya kawo hargitsi. Ya kuma gargadi cewa duk wanda hukumar ta kama da hannu a irin wadannan ayyuka, za a gurfanar da shi a kotu domin ya fuskanci hukunci daidai da laifin da ya aikata.

Comments

Popular posts from this blog

Zazzau Emir’s Defamation Case: Court Bars Claimant Over Non-Compliance, Adjourns Proceedings

Alleged 419 Case: Senator Abdu Kwari in Fresh Court Battle Over Property Deal

Maradin, Dan Saran and Wakilin Watsa Labaran Zazzau Honour Loyal Aides with Traditional Titles