Iyalan El-Rufai sun buƙaci a sake shi ba tare da ɓata lokaci ba
Iyalan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai sun bayyana cigaba da riƙe shi da ake yi a matsayin karan-tsaye ga dokokin Najeriya, sannan suka yi zargin ana amfani da hukumar yaƙi da cin hanci a matsayin karen farauta domin muzgunawa ƴan hamayya.
Iyalan sun bayyana haka ne a wata sanarwa da Bello El-Rufai ya fitar a madadinsu a ranar Juma'a, 6 ga watan Maris, inda ya bayyana tsare mahaifin nasu da "saɓa doka."
"Har yau Juma'a 6 ga watan Maris, Nasir El-Rufai na tsare a hannun ICPC wanda ba bisa doron doka suke yi ba. Muna sanar da al'umma cewa babu dokar da ta amince a cigaba da tsare shi."
Iyalan sun ce an fara tsare tsohon gwamnan ne a ranar 18 ga Fabrairun 2026, "sannan hukumar ta nemi izinin tsare shi na kwana 14. Amma har yanzu da kwanakin suka ƙare, ICPC ba ta kai shi kotu ba, sannan tana cigaba da tsare shi. Wannan karan-tsaye ne ga dokokin Najeriya, saboda hukumar ta gaza wajen gabatar da shi a kotu, ko kuma ta sake shi."
Bello ya bayyana a sanarwar cewa cigaba da tsare El-Rufai ya ƙara tabbatar "abin da muka daɗe muna fargaba cewa ana amfani na hukumar ne domin muzgunawa abokan hamayya. Don haka ne muke nema da a sake shi ba tare da ɓata lokaci ba."
Comments
Post a Comment