Jiragen yaƙi da dama na Amurka sun yi hatsari a Kuwait - Ma'aikatar tsaro
Ma’aikatar Tsaro ta ƙasar Kuwait ta sanar da cewa jiragen yaƙi da dama na rundunar sojin Amurka sun yi haɗari a safiyar yau a ƙasar da ke gabas ta tsakiya kamar yadda jaridar TheCable ta wallafa.
Har yanzu ba a san abin da ya haddasa haɗarin ba, amma kakakin ma’aikatar tsaron ya tabbatar a cikin wata sanarwa cewa ma’aikatan jiragen sun tsira gaba ɗaya ba tare da wata matsala ba.
Ba a kuma bayyana adadin jiragen yaƙin ko yawan ma’aikatan da abin ya shafa ba.
A cewar sanarwar, jami’an tsaro sun kwashe ma’aikatan jiragen tare da kai su asibiti domin kula da lafiyarsu bayan an kammala aikin ceto da bincike.
Sanarwar ta bayyana cewa yanayin lafiyar ma’aikatan “yana da kyau kuma yana da daidaito.”
“Jami’an da abin ya shafa na ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin,” in ji sanarwar.
Tun da fari, wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta ya nuna wani jirgin yaƙi yana cin wuta kafin ya faɗi a sararin samaniyar Kuwait, kusa da wani sansanin sojin Amurka.
Ba a san dalilin faɗuwar jirgin ba ko kuma rundunar sojin da jirgin ya ke ba, amma binciken da kafar yaɗa labarai ta CNN ta gudanar ya nuna cewa jirgin mai injina biyu da aka gani a bidiyon ya yi kama da jirgin yaƙi na F-15E Strike Eagle na Amurka. L
Ƙasar Iran ta ɗauki alhakin harbo jirgin.
Ya zuwa yanzu, sojojin Amurka uku sun mutu, yayin da wasu biyar suka jikkata tun bayan da Amurka da Isra’ila suka kaddamar da hare-haren haɗin gwiwa kan Iran a safiyar ranar Asabar.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sha alwashin ɗaukar fansa kan mutuwar sojojin, amma ya yi gargaɗin cewa akwai yiyuwar ƙarin asarar rayuka kafin yaƙin ya zo ƙarshe.
Comments
Post a Comment