Majalisa ta gayyaci Kyari kan zargin ɓatan maƙudan kuɗi a NNPCL


Kwamitin kula da asusun gwamnati na Majalisar Dattawan Najeriya ya gayyaci tsohon shugaban Kamfanin Man Fetur na ƙasar, Mele Kyari, domin ya yi bayani kan zargin wasu kuɗaɗe da yawansu ya kai naira tiriliyan 210 da ake cewa ba a yi cikakken bayanin yadda aka kashe su ba tsakanin shekarun 2017 zuwa 2023, lokacin da yake jagorantar kamfanin.

An gayyaci Kyari tare da tsohon babban jami’in kula da harkokin kuɗi na kamfanin, Umar Ajia Isa, da kuma tsohon babban manajan kula da harkokin zuba jari na kamfanin, Bala Wunti.

Shugaban kwamitin, Sanata Aliyu Wadada, ne ya bayar da umarnin gayyatar a ranar Alhamis bayan da kwamitin ya duba rahotannin binciken kuɗi da suka shafi kamfanin NNPCL.

Kwamitin ya kuma yi gargaɗin cewa zai iya fitar da sammacin kama waɗanda abin ya shafa idan suka gaza bayyana a gaban kwamitin a ranar da za a sanar nan gaba.

Sanata Wadada ya bayyana wannan matsaya ta kwamitin ne yayin da yake yi wa manema labarai ƙarin bayani bayan kammala taron kwamitin.

A cewarsa, ana sa ran tsoffin shugabannin kamfanin za su bayyana tare da shugabancin kamfanin na yanzu ƙarƙashin jagorancin sabon Babban Darakta, Bayo Ojulari, da kuma masu binciken kuɗi na waje da suka yi aiki da kamfanin a lokacin da ake magana a kai.

Comments

Popular posts from this blog

Zazzau Emir’s Defamation Case: Court Bars Claimant Over Non-Compliance, Adjourns Proceedings

Alleged 419 Case: Senator Abdu Kwari in Fresh Court Battle Over Property Deal

Maradin, Dan Saran and Wakilin Watsa Labaran Zazzau Honour Loyal Aides with Traditional Titles