Matashi daga jihar Kano ya ƙaddamar da takarar kujerar shugaban matasa na jam'iyyar APC na ƙasa



Wani dan jam’iyyar APC, Bashir Suwaid, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Shugaban Matasan jam’iyyar na kasa.

Suwaid, wanda dan asalin jihar Kano ne, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, inda ya ce ya dauki matakin ne bayan tuntuba da shugabannin jam’iyya da masu ruwa da tsaki na matasa a fadin kasar.

Da yake jawabi ga shugabannin jam’iyya da ‘yan jarida, Suwaid ya ce ya zama dole a kara karfafa bangaren matasan APC tare da inganta tsarinsa domin amfani da karfi da gudunmawar matasa a duk fadin kasar.

Ya ce matasan jam’iyyar sun taka muhimmiyar rawa wajen tattara goyon baya da kuma karfafa tsarin jam’iyyar tun daga matakin mazabu har zuwa kasa baki daya.

Suwaid ya kuma jaddada cewa matasan Nijeriya a yanzu sun fi ilimi da hadin kai, kuma suna da sha’awar ba da gudunmawa ga ci gaban kasa.

Ya kara da cewa ya shiga takarar ne cikin kaskantar da kai tare da girmama sauran masu neman kujerar, yana mai alkawarin yi wa jam’iyyar aiki da gaskiya idan aka ba shi dama.

A cewarsa, da goyon bayan shugabannin jam’iyya da matasa a fadin kasa, bangaren matasan APC zai kara karfi da hadin kai gabanin zabukan siyasa masu zuwa.

Comments

Popular posts from this blog

Zazzau Emir’s Defamation Case: Court Bars Claimant Over Non-Compliance, Adjourns Proceedings

Alleged 419 Case: Senator Abdu Kwari in Fresh Court Battle Over Property Deal

Maradin, Dan Saran and Wakilin Watsa Labaran Zazzau Honour Loyal Aides with Traditional Titles