Mutane 3 da za su jagoranci Iran bayan rasuwar jagoran jamhuriyar musulunci, Ayatollah Ali Khamenei
Kwamitin mutune uku zai jagoranci ƙasar Iran na wucin gadi bayan rasuwar Jagoran Jamhuriyar Musulunci, Ayatollah Ali Khamenei.
Rahotanni daga kafafen yaɗa labarai na gwamnatin Iran sun bayyana cewa kwamitin zai ƙunshi Shugaban Ƙasa, Masoud Pezeshkian, shugaban ɓangaren shari’a, Gholamhossein Mohseni Ejei, da kuma wani mamba daga Majalisar Masu Tsaron Tsarin Mulki (Guardian Council). Za su riƙe ragamar mulki a lokacin miƙa mulki.
Mutanen uku za su karɓi ayyukan marigayi Khamenei har sai Majalisar Kwararru (Assembly of Experts), wadda ta ƙunshi manyan malamai 88 masu tasiri, ta zaɓi sabon jagora.
Dokar ƙasar Iran ta tanadi cewa Majalisar Kwararru dole ne ta zaɓi sabon Jagoran Koli cikin gaggawa.
Har yanzu ba a bayyana wanda zai gaji Khamenei ba, wanda aka kashe a hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran a ranar Asabar.
Comments
Post a Comment