Najeriya za ta karɓi maganin rigakafin HIV a watan Maris – NACA


Hukumar dakile yaduwar cuta mai karya garkuwar jiki (NACA) ta sanar da cewa Najeriya za ta karɓi maganin rigakafin cutar HIV mai suna Lenacapavir a watan Maris 2026.

A cikin wata gajeriyar sanarwa da Shugabar Hulɗa da Jama’a ta hukumar, Toyin Aderibigbe, ta fitar a ranar Litinin, ta bayyana cewa hukumar ta samu amincewar doka daga hukumar NAFDAC domin shigo da maganin cikin ƙasa.

Lenacapavir magani ne da ake yi ta allura sau biyu kacal a shekara, wanda hakan ya sa ya fi sauƙi idan aka kwatanta da magungunan rigakafin da ake sha kullum. Gwaje-gwajen kimiyya sun nuna cewa maganin ya nuna kashi 100 cikin 100 na kariya daga kamuwa da cutar HIV a binciken asibiti.

Sanarwar ta ce gwamnatin Najeriya na ci gaba da shirye-shiryen fara amfani da maganin a matsayin rigakafin kafin kamuwa da cuta (PrEP), a wani ɓangare na ƙudurin gwamnati na ƙarfafa yaƙi da HIV da kuma hanzarta rage yaduwar cutar a ƙasa.

Hukumar ta kuma bayyana cewa ana sa ran maganin zai kasance a Najeriya da wasu ƙasashe 119 masu ƙarami da matsakaicin ƙarfin tattalin arziki, a farashi mai sauƙi na dala 40 ga kowane mutum a shekara, sakamakon yarjejeniyar bayar da lasisi ga kamfanonin da ke ƙera magungunan irinsu (generic manufacturers).

Comments

Popular posts from this blog

Zazzau Emir’s Defamation Case: Court Bars Claimant Over Non-Compliance, Adjourns Proceedings

Alleged 419 Case: Senator Abdu Kwari in Fresh Court Battle Over Property Deal

Maradin, Dan Saran and Wakilin Watsa Labaran Zazzau Honour Loyal Aides with Traditional Titles