Sallar Juma'a ta gagari kauyuka kusan 10 a jihar Katsina ta dalilin ayyukan barayin daji

Fargaba ta mamaye wasu kauyuka a jihar Katsina bayan wani mummunan rikici tsakanin kungiyoyin ‘yan bindiga da ya tilasta wa mazauna sama da kauyuka goma dakatar da sallar Juma’a saboda tsananin harbe-harben bindiga da ya dauki tsawon sa’o’i.

Manema labarai  sun ruwaito cewa rikicin ya faru ne a yankunan karkara da ke iyaka da kananan hukumomin Musawa, Kankara da kuma Malumfashi, inda aka yi musayar wuta tsakanin kungiyoyin ‘yan bindiga na tsawon lokaci, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin tsananin fargaba.

Rahotanni sun ce tun kafin lokacin sallar Juma’a, wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kai farmaki a garin Dangani da rana tsaka, inda suka shiga garin kan babura fiye da 70.

Maharan sun lalata shagunan sayar da wayoyi tare da kwace wayoyin da ake cajawa a wuraren caji da kuma wadanda suka samu a hannun mazauna yankin.

Comments

Popular posts from this blog

Zazzau Emir’s Defamation Case: Court Bars Claimant Over Non-Compliance, Adjourns Proceedings

Alleged 419 Case: Senator Abdu Kwari in Fresh Court Battle Over Property Deal

Maradin, Dan Saran and Wakilin Watsa Labaran Zazzau Honour Loyal Aides with Traditional Titles