Sanata Wamakko ya rabawa marayu 10,000 tallafin Naira dubu daya, daya kowannen su a Sokoto
Sanata Wamakko ya rabawa marayu 10,000 tallafin Naira dubu daya, daya kowannen su a Sokoto
Tsohon gwamnan Jihar Sokoto, Sanata Aliyu Wamakko, ya bayar da tallafin naira miliyan 10 da kuma kala 100 na kayan sawa domin tallafa wa marayu da sauran marasa galihu gabanin bikin Sallah.
An miƙa tallafin ne ta hannun hukumar zakka da Waqafi ta Jihar Sokoto (SOZEA), inda shugaban hukumar, Lawal Maidoki, ya karɓa a ranar Asabar a Sokoto.
Sanata Wamakko, mai wakiltar Sokoto ta Arewa a majalisar dattawa, ya ce tallafin na da nufin taimaka wa kusan mutane 10,000, musamman marayu, domin su samu damar gudanar da bikin Sallah cikin farin ciki.
Ya bayyana cewa tallafin wani ɓangare ne na ƙoƙarin taimaka wa marasa galihu musamman a cikin watan Ramadan da lokacin Sallah.
A nasa jawabin, shugaban hukumar SOZEA, Lawal Maidoki, ya gode wa sanatan kan wannan taimako, yana mai cewa za a raba tallafin yadda ya dace ga waɗanda aka nufa da shi.
Comments
Post a Comment