Tiani ya karɓi rahoton bincike kan illar hakar Uranium a Arlit
Shugaban mulkin sojin Jamhuriyar Nijar, Janar Abdurahamane Tiani, ya karɓi binciken kwamitin ƙwararrun masana da aka kafa domin binciken tasirin ayyukan hakar uranium a yankin Arlit, a ranar 28 ga Fabrairu, 2026.
Bayan fiye da shekara ɗaya da rabi ana gudanar da binciken, kwamitin ya miƙa taƙaitaccen rahoton sakamakon bincikensa ga shugaban.
A cewar mai ba Shugaban shawara na musamman, sakamakon binciken ya nuna cewa ayyukan kamfanin Orano da suka shafe fiye da shekaru 50 a yankin sun bar manyan matsaloli masu tsanani, musamman ga tsarin halittu da kuma muhalli gaba ɗaya.
Comments
Post a Comment