Ƴan majalisar APC na Bauchi sun ziyarci Gwamnan Bauchi a yayin da yake shirin sauya sheƙa


Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya karɓi bakuncin wasu ’yan majalisar wakilai na jam’iyyar APC daga jihar a gidansa da ke Abuja, yayin da ake rade-radin shirin ficewarsa daga jam’iyyar PDP kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.

Rahotanni sun ce gwamnan ya gana da ’yan majalisar ne domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan shirin sauya sheƙarsa zuwa jam’iyya mai mulki. Bayan ganawar, ɗan majalisar mai wakiltar mazaɓar Toro, Dabo Ismail, ya bayyana cewa an gayyace su ne domin tattauna sabbin sauye-sauyen siyasa da ke gudana a ƙasar, musamman a jihar Bauchi.

Ya ce sun tattauna muhimman batutuwa da suka shafi ci gaban jihar, tare da samun wasu matsaya masu kyau. Ya ƙara da cewa nan gaba kaɗan za su bayyana matsayarsu, yayin da za su ci gaba da tuntuɓar sauran masu ruwa da tsaki tare da sanar da su sakamakon ganawar.

A baya, a ranar 1 ga Afrilu, Bala Mohammed ya karɓi shugabannin APC na ƙasa da wasu gwamnoni a Bauchi, ciki har da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Nentawe Yilwatda, da gwamnan Kano, Abba Yusuf.

Kafin wannan ganawa, gwamnan ya kuma karɓi wasu ’yan jam’iyyar ADC, inda ya bayyana cewa yana duba yiwuwar komawa APC tare da magoya bayansa. Sai dai ya nuna cewa APC ba ta nuna cikakken shiri na karɓarsa ba, yana mai cewa ADC na iya zama mafita a gare shi da mabiyansa.

A gefe guda, wasu jiga-jigan APC a Bauchi sun buƙaci shugabancin ƙasa na jam’iyyar da ya tuntube su a duk wata tattaunawa kafin a amince wa da shigar Bala Mohammed cikin jam’iyyar.

Comments

Popular posts from this blog

Zazzau Emir’s Defamation Case: Court Bars Claimant Over Non-Compliance, Adjourns Proceedings

Alleged 419 Case: Senator Abdu Kwari in Fresh Court Battle Over Property Deal

Maradin, Dan Saran and Wakilin Watsa Labaran Zazzau Honour Loyal Aides with Traditional Titles