Babu hannun Tinubu a rikicin ADC, in ji Onanuga

Mai magana da yawun Shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba shi da hannu a rikicin cikin gida da ke addabar ADC, yana mai cewa matsalolin da jam’iyyar ke fuskanta “su suka jawo wa kansu.”

Onanuga ya yi wannan bayani ne yayin da yake mayar da martani kan zarge-zargen da ake yi cewa akwai sa hannun gwamnatin tarayya a rikicin jam’iyyar.

Ya kuma soki tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, inda ya ce ya bar jam’iyyarsa cikin rikici ba tare da warware matsalolinta ba. A cewarsa, Obi bai nuna ƙwarewa wajen gina jam’iyya mai ƙarfi ko ingantaccen tsari ba.

Haka zalika, Onanuga ya zargi tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da hannu wajen sayen jam’iyyar ADC, yana mai cewa wannan mataki ne ya haifar da rikice-rikicen da jam’iyyar ke fama da su a halin yanzu.

A ƙarshe, ya ce tasirin siyasar Peter Obi a zaɓen 2027 zai dogara ne kacokan kan samun tikitin tsayawa takara, yana mai ƙara da cewa nasarar da ya samu a zaɓen 2023 ba lallai ba ne ta maimaitu a zaɓen mai zuwa.

Comments

Popular posts from this blog

Zazzau Emir’s Defamation Case: Court Bars Claimant Over Non-Compliance, Adjourns Proceedings

Alleged 419 Case: Senator Abdu Kwari in Fresh Court Battle Over Property Deal

Maradin, Dan Saran and Wakilin Watsa Labaran Zazzau Honour Loyal Aides with Traditional Titles