Bankin Duniya ya amince da rancen dala miliyan 500 domin tallafa wa ƙananan manoma a Najeriya.
Bankin duniya, World Bank ya bayyana cewa ya amince da bayar da rancen dala miliyan 500 ga Najeriya ta hannun International Development Association (IDA), domin tallafawa aiwatar da shirin noma na AGROW (Nigeria Sustainable Agricultural Value-Chains for Growth).
A cikin sanarwar da bankin ya fitar, ya ce shirin yana da nufin ƙara yawan amfanin gona na ƙananan manoma, bunƙasa samar da amfanin gona da kasuwancin su da kuma samar da ayyukan yi.
Bankin ya bayyana cewa har yanzu manoma da dama na rayuwa ne a matakin noma na kai-da-kai (subsistence farming), yayin da ƙarancin abinci mai gina jiki ke shafar miliyoyin ’yan Najeriya.
Shirin AGROW zai tallafa wa kamfanonin noma (agribusiness) da suka yi alƙawarin sayen kayan amfanin gona daga ƙananan manoma, ta hanyar tsarin tallafin kuɗi na hadin gwiwa (matching grants).
Comments
Post a Comment