Dakarun sojin Nijeriya sun kashe 'yan ta’adda 24 a Yobe

Dakarun sojin Nijeriya sun kashe 'yan ta’adda 24 a Yobe



Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Gabas, Operation Hadin Kai, sun dakile wani hari da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka kai a garin Kukareta da ke jihar Yobe , inda suka kashe mutum 24 daga cikin maharan bayan fafatawa mai tsanani.

Rahotanni sun ce harin ya faru ne da sanyin safiyar Alhamis, inda maharan suka yi ƙoƙarin kwace sansanin sojoji da ke yankin. Fafatawar ta ɗauki kusan awa uku kafin sojojin su samu nasarar murƙushe harin.

Jami’in yaɗa labarai na rundunar, Sani Uba, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce sojojin sun mayar da martani cikin gaggawa tun bayan fara harin daga tsakar dare zuwa kusan ƙarfe 3 na safe.

Ya ƙara da cewa dakarun sun haɗa kai wajen kai farmaki da kare kansu a lokaci guda, abin da ya tilasta maharan ja da baya cikin ruɗani.

A cewarsa, an kashe ‘yan ta’adda 24 yayin artabun, sannan sojojin sun kwato makamai masu yawa daga hannunsu. Daga cikin kayayyakin da aka ƙwato akwai bindigogi kirar AK-47 guda 18, manyan bindigogi guda uku, bindigogin PKT guda biyu, roka guda uku, mortar guda biyu, da kuma gurneti guda huɗu tare da aljihunan harsasai da dama.

Sai dai ya bayyana cewa sojoji biyu sun ji rauni a yayin musayar wuta, kuma an riga an kai su asibiti domin kula da lafiyarsu, yayin da wata motar sulke ta lalace.

Comments

Popular posts from this blog

Zazzau Emir’s Defamation Case: Court Bars Claimant Over Non-Compliance, Adjourns Proceedings

Alleged 419 Case: Senator Abdu Kwari in Fresh Court Battle Over Property Deal

Maradin, Dan Saran and Wakilin Watsa Labaran Zazzau Honour Loyal Aides with Traditional Titles