Ganduje bashi da ikon bani umarni a APC saboda nine jagoran jam'iyyar a Kano - Abba Gida-Gida



Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ba zai iya ba shi umarni ba, yana mai cewa shi ne jagoran jam’iyyar a jihar.

Yusuf ya yi wannan bayani ne yayin da yake mayar da martani kan sukar da ake yi masa biyo bayan sauya shekarsa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC, inda ya jaddada cewa bai yi wa tafiyar Kwankwasiyya butulci ba.

Da yake jawabi a wani taro da ya yi da mawallafa waƙoƙin sa a jiya a Kano, gwamna Abba ya kara da cewa sauya shekarsa ta samo asali ne sakamakon rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar NNPP.

Gwamnan ya kuma ce duk da girmamawar da yake yi wa Ganduje, ba zai amince ya riƙa juya shi ba.

A cewar gomna Yusuf “Abin da ke tsakaninmu ni da Ganduje girmama juna ne. Amma ba shi da ikon ba ni umarni, domin ni ne jagora,”

Comments

Popular posts from this blog

Zazzau Emir’s Defamation Case: Court Bars Claimant Over Non-Compliance, Adjourns Proceedings

Alleged 419 Case: Senator Abdu Kwari in Fresh Court Battle Over Property Deal

Maradin, Dan Saran and Wakilin Watsa Labaran Zazzau Honour Loyal Aides with Traditional Titles