Gwamnan Kano ya yi alƙawarin magance matsalar ruwa



Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sha alwashin magance matsalar ƙarancin ruwa a jihar, inda ya kai ziyarar duba dukkan matatun ruwa domin tantance halin da suke ciki.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mustapha Muhammad, ya fitar, ya ce ziyarar na da nufin gano matsalolin da ke hana samar da wadataccen ruwa a wasu sassan jihar da kuma nemo hanyoyin warware su.

Gwamnan ya fara ziyarar ne daga matatar ruwan Tamburawa, inda ya duba muhimman kayan aiki da bututun rarraba ruwa. 

An gano matsaloli da suka haɗa da zubewar ruwa daga bututu, lalacewar injuna da kuma tsofaffin kayan aiki.

Ya jaddada kudirin gwamnatinsa na gyara dukkan sassan da suka lalace domin inganta samar da ruwa ga al’umma.

Haka kuma, gwamnan ya bayyana cewa za su haɗa kai da kamfanin kasar Sin na CGC domin samar da mafita mai dorewa ga matsalar ruwa a jihar.

Ya ƙara da cewa samar da tsaftataccen ruwan sha mai inganci na daga cikin manyan manufofin gwamnatinsa, yana mai tabbatar da cewa za a yi duk mai yiwuwa domin kowane ɗan ƙasa ya samu ruwa mai kyau.

Comments

Popular posts from this blog

Zazzau Emir’s Defamation Case: Court Bars Claimant Over Non-Compliance, Adjourns Proceedings

Alleged 419 Case: Senator Abdu Kwari in Fresh Court Battle Over Property Deal

Maradin, Dan Saran and Wakilin Watsa Labaran Zazzau Honour Loyal Aides with Traditional Titles