Gwamnatin tarayya na shirin sassauta bashin kamfanonin jiragen sama
Gwamnatin tarayya na shirin sassauta bashin kamfanonin jiragen sama
Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin rage ko ma yafewa kamfanonin jiragen sama wasu daga cikin basussukan da suke bin hukumomin kula da harkokin jiragen sama, domin rage musu nauyin da suka shiga sakamakon tashin farashin man jirgi (Jet A1).
Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya ce Shugaban ƙasa na duba yiwuwar ba da rangwame kan basussukan da hukumomi kamar Hukumar Kula da Sararin Samaniya (NAMA), Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Tarayya (FAAN) da kuma Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) suke bin kamfanonin.
Ya ƙara da cewa za a kafa wani kwamiti na musamman da zai duba haraji da kudaden da ake ɗora wa tikitin jiragen sama na cikin gida, domin rage tsadar sufuri ga ‘yan ƙasa.
A nasa ɓangaren, shugaban kamfanin jiragen sama na Air Peace, Allen Onyema, ya bayyana cewa matsalar da kamfanonin ke fuskanta ta samo asali ne daga hauhawar farashin man Jet A1, wanda ya ƙaru da sama da kashi 300 cikin ɗari a ‘yan shekarun nan.
Onyema ya kuma nuna damuwa kan tsadar bashin da kamfanoni ke karɓa a Najeriya, wanda ya kai tsakanin kashi 30 zuwa 35 cikin ɗari, yana mai cewa hakan ya fi tsanani idan aka kwatanta da ƙasashen waje inda ribar bashin ke kusan kashi 3 cikin ɗari kacal.
A baya dai, kamfanonin jiragen sama sun yi barazanar dakatar da ayyukansu saboda tsadar mai, sai dai daga bisani sun dakatar da wannan shiri na ɗan lokaci bayan roƙon gwamnati, yayin da suke jiran matakan da za a ɗauka domin magance matsalar.
Comments
Post a Comment