Gwamnatin tarayya ta ware sama da Naira Biliyan 1 a kasafin kuɗi don shari'o'in da suka shafi ta'addanci
Gwamnatin tarayya ta ware kimanin Naira biliyan 1.37 a kasafin kuɗin shekarar 2026 domin gurfanar da ‘yan ta’addan Boko Haram da sauran masu aikata laifukan ta’addanci, adadin da ya nuna ƙaruwa mai yawa idan aka kwatanta da Naira miliyan 530 da aka ware a shekarar 2025, wanda ya kai kusan kashi 159 cikin ɗari kamar yadda jaridar PUNCH ta rawaito.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya rattaba hannu kan kasafin kuɗin 2026 na Naira tiriliyan 68.32, inda aka keɓe Naira tiriliyan 5.41 domin harkokin tsaro.
Ƙarin kuɗin na nuni da cewa gwamnati na ƙara maida hankali wajen yaƙi da matsalar rashin tsaro da kuma tabbatar da an gurfanar da masu laifi a gaban kotu.
Rahotanni sun nuna cewa kuɗin da aka ware domin shari’o’in ta’addanci ya zama wani muhimmin kaso a cikin kuɗaɗen da ma'aikatar shari'a ke kashewa.
A nasa ɓangaren, Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, ya buƙaci kotuna da su hanzarta sauraron shari’o’in da suka shafi ta’addanci domin tallafa wa ƙoƙarin ƙasa wajen shawo kan matsalar tsaro.
Masana sun jaddada muhimmancin tabbatar da gaskiya da rikon amana wajen kashe irin wannan kuɗi, tare da buƙatar inganta tsaro a gidajen yari da kuma hanzarta tafiyar da shari’o’i domin samun sakamako mai inganci.
Comments
Post a Comment