Gyaran layin wutar lantarki: Jihohi 7 za su fuskanci rashin wuta na tsawon makonni 6
Kamfanin Kula da Wuyar Lantarki mai zaman kansa na ƙasa (NISO) ya sanar da cewa jihohi bakwai za su fuskanci ƙarancin wutar lantarki na tsawon makonni shida sakamakon wani shirin gyara da aka tsara a layin wutar Jos–Gombe mai ƙarfin 330kV.
A wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Alhamis, kamfanin ya ce za a fara aikin daga ranar 9 ga Afrilu zuwa 22 ga Mayu, 2026.
NISO ya bayyana cewa za a riƙa samun katsewar wutar ne duk mako daga ranar Alhamis zuwa Lahadi, tsakanin ƙarfe 9:00 na safe zuwa 6:00 na yamma, domin baiwa aikin girka wayar sadarwa ta fibre optic damar gudana a kan layin.
Jihohin da abin zai shafa sun haɗa da Plateau, Gombe, Bauchi, Borno, Adamawa, Taraba da Yobe.
Kamfanin ya ce wannan gyara na daga cikin ƙoƙarin sabunta tsarin lantarki na ƙasa domin inganta aiki ta hanyar amfani da sabbin fasahohi kamar tsarin SCADA, tsarin sarrafa makamashi, da kuma ingantaccen sadarwa.
Comments
Post a Comment