Kotu ta bada belin mutanen da su ka ci zarafin Farfesa Umar Sani Fagge


Kotun majistare mai lamba 53 da ke zamanta a Norman’s Land a Kano ta bada belin wasu mutane uku da ake zargi da cin zarafin Sheikh Farfesa Umar Sani Fagge.

Manema labarai sun rawaito cewa, an gurfanar da Adamu Adamu da Salihu Bala da Hassan Umar a gaban alƙalin kotun, Mustapha Sa’ad Datti bisa tuhume-tuhume da su ka hada da hadin baki domin aikata laifi da cin zarafi da kuma tada tarzoma.

A yayin zaman kotun a yau Alhamis, alƙalin ya saurari karar inda wadanda ake zargin su ka musanta tuhume-tuhumen.

Daga bisani ne lauyansu ya nemi a bads belin su.

Kotun ta amince da bayar da belin kan sharadin naira dubu hamsin ga kowanne daga cikinsu tare da samar da masu tsaya musu biyu, daya darakta daya kuma malamin jami’a.

Kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 28 ga Afrilu 2026 domin ci gaba da shari’a.

Ana zarginsu da yin kalaman ɓatanci a wani taron siyasa a Kwaciri inda a taron wani Isyaku Mai Fenti ya ce, Akuyar Kwaciri ta fi Malam Umar Sani Fagge, kuma ya wallafa bayanin a shafinsa.

Sai dai ana zargin shi Isyaku Mai Fenti ya gudu.

Comments

Popular posts from this blog

Zazzau Emir’s Defamation Case: Court Bars Claimant Over Non-Compliance, Adjourns Proceedings

Alleged 419 Case: Senator Abdu Kwari in Fresh Court Battle Over Property Deal

Maradin, Dan Saran and Wakilin Watsa Labaran Zazzau Honour Loyal Aides with Traditional Titles