Kotu ta umarci a tsare waɗanda ake zargi da shirin juyin mulki a hannun DSS
Kotu ta umarci a tsare waɗanda ake zargi da shirin juyin mulki a hannun DSS
Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare wasu mutane shida da ake zargi da hannu a shirin juyin mulki a hannun hukumar tsaro ta farin kaya Kaya (DSS), bayan an gurfanar da su kan tuhume-tuhume guda 13 da suka shafi zargin ta’addanci.
A zaman kotun da aka fara da misalin ƙarfe 1:46 na rana a ranar Laraba, Babban Lauyan tarayya, Lateef Fagbemi (SAN), ya shaida wa kotun cewa an shirya tuhumar, inda ya nemi a karanta wa waɗanda ake zargin laifukan da ake tuhumarsu da su.
Sai dai shari’ar ta ɗan tsaya na ɗan lokaci bayan wanda ake tuhuma na uku ya bayyana cewa lauyansa ba ya nan saboda rashin lafiya, yayin da lauyan wanda ake tuhuma na shida ya ce wanda yake karewa na fahimtar harshen Larabci da Hausa kaɗai, lamarin da ya sa kotu ta dakatar da zaman domin samar da mai fassara.
Da aka koma zaman kotun da misalin ƙarfe 2:18 na rana, dukkanin waɗanda ake tuhumar sun ki amsa laifukansu inda suka musanta zarge-zargen, tare da cewa ba su aikata ba.
Bayan haka, masu gabatar da ƙara sun nemi kotu ta bayar da umarnin ci gaba da tsare su a hannun DSS tare da gaggauta sauraron shari’ar. Yawancin lauyoyin masu kare waɗanda ake tuhuma ba su yi adawa da wannan buƙata ba, sai dai lauyan wanda ake tuhuma na farko ya nuna aniyar shigar da buƙatar beli.
A hukuncin da ya yanke, alkalin kotun ya amince da buƙatar gaggauta sauraron shari’ar, tare da umartar a ci gaba da tsare waɗanda ake tuhumar a hannun DSS, amma su rika samun damar ganawa da lauyoyinsu.
Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 27 ga Afrilu, 2026, domin fara cikakken sauraron ƙarar.
Comments
Post a Comment