Kotu ta yanke wa wani mutum ɗaurin rai-da-rai bisa yi wa ƴar shekara 9 fyaɗe a Jigawa
Kotu ta yanke wa wani mutum mai suna Bashir A. Umar hukuncin ɗaurin rai-da-rai bayan an kama shi da laifin yi wa yarinya ƴar shekara 9 fyaɗe har ya raunata ta a Jihar Jigawa.
Tun a bara kotu ta samu Umar da laifin, sannan ta yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai kan laifin fyade, da kuma ɗaurin shekaru 7 kan laifin jikkata yarinyar.
Haka kuma, kotun ta umarce shi ya biya diyyar naira miliyan 1 ga yarinyar.
Gwamnatin jihar ta yaba da hukuncin, tana cewa adalci ya tabbata.
Gwamnatin ta kuma kula da lafiyar yarinyar tare da taimaka wa iyayen ta da kyautar gida.
Comments
Post a Comment