Kotun ɗaukaka ƙara ta umarci a kawo Sheikh Abduljabbar domin ya kare kansa


Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Kano ta bayar da umarni ga hukumar kula da gidajen gyaran hali ta ƙasa da ta gabatar da Sheikh Abduljabbar Kabara a gaban kotu domin ci gaba da sauraron ƙarar da ya ɗaukaka.

Sheikh Abduljabbar, malamin addinin Musulunci, na tsare a gidan yari ne bayan wani hukunci da Ƙaramar Kotun Shari’a ta yanke, inda ta same shi da laifin batanci tare da yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

A yayin zaman kotun a ranar Litinin, jagoran alkalai, mai shari’a Mohammed Lawal-Shuaibu, ya bayyana cewa tun da wanda ya shigar da ƙarar ya yi hakan da kansa ba tare da lauya ba, dole ne ya bayyana a gaban kotu domin kare kansa da hujjojinsa.

Sauran alkalan da suka zauna tare da shi sun haɗa da Mai shari’a Abubakar Mu’azu-Lamido da Mai shari’a Ahmad Ramat-Mohammed.

Alkalin ya ce, “Tunda mai ƙara ya shigar da ƙarar da kansa ba tare da wakilcin lauya ba, wajibi ne ya bayyana a gaban kotu da kansa. Haka kuma, kasancewar yana tsare, an umarci hukumar gidan yari da ta gabatar da shi a ranar 23 ga Afrilu, 2026 domin ci gaba da sauraron ƙarar.”

Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 23 ga Afrilu domin ci gaba da sauraron ƙarar.

Tun da farko, lokacin da aka kira shari’ar, babu ɓangarorin da suka halarta ko wakilansu a kotu.

A wannan lokaci ne wani mutum mai suna Usman Malam-Hussaini ya tashi ya sanar da kotu cewa Sheikh Abduljabbar ya aiko shi da wasiƙa domin neman a mayar da shi Kano daga gidan yarin Kuje, don samun damar duba takardunsa cikin sauƙi.

Sai dai alkalin ya gayyaci Babban Lauyan Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru-Maude (SAN), da ya bayyana a gaban kotu, tare da ɗage sauraron shari’ar na ɗan lokaci.

Daga bisani, lokacin da aka sake kiran shari’ar, Mataimakin Daraktan Gurfanar da Ƙara na Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano, Barista Zahradeen Kofar-Mata, ya shaida wa kotu cewa Babban Lauyan jihar ba ya cikin koshin lafiya, kuma ya nemi a miƙa uzurinsa ga kotu saboda rashin halarta.

Ya ƙara da cewa an bai wa wani lauya mai zaman kansa shari’ar, sannan ya danganta jinkirin da aka samu da wata tangarda a sashen rajista.

Sai dai alkalin ya nuna rashin jin daɗinsa kan rashin halartar Babban Lauyan jihar, yana mai cewa hakan rashin girmama kotu ne, kafin daga bisani ya ɗage shari’ar zuwa ranar da aka tsara.

Comments

Popular posts from this blog

Zazzau Emir’s Defamation Case: Court Bars Claimant Over Non-Compliance, Adjourns Proceedings

Alleged 419 Case: Senator Abdu Kwari in Fresh Court Battle Over Property Deal

Maradin, Dan Saran and Wakilin Watsa Labaran Zazzau Honour Loyal Aides with Traditional Titles