Kwankwaso ya taya tsohon mataimakin gwamnan Kano, Gwarzo murnar shiga jam'iyyar ADC



Jagoran ɗarikar Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya taya tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo murnar shiga jam'iyyar ADC a hukumance.

Manema labarai sun rawaito cewa dandazon magoya baya ne su ka halarci bikin yankar katin jam'iyyar ADC a mazaɓar sa ta Gwarzo a jiya Lahadi.

A wani sako da ya wallafa a shafin sa na Facebook, Kwankwaso ya baiyana gagarumin taron ya kara wa jam'iyyar kwarin gwiwar samun nasarori a nan gaba.

"Ina taya Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, murna da gaske bisa shawarar da ya yanke na shiga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).

" Babban taron tarba da aka yi jiya a Garin Gwarzo ba wai kawai ya ƙara mana karfi ba ne tare da dimbin gogewarsa, har ma ya kara mana azama da sabuwar himma a cikin jam’iyyar.

"Barka da dawowa gida, Mai Girma Aminu Abdussalam Gwarzo. – RMK," in ji Kwankwaso.

Comments

Popular posts from this blog

Zazzau Emir’s Defamation Case: Court Bars Claimant Over Non-Compliance, Adjourns Proceedings

Alleged 419 Case: Senator Abdu Kwari in Fresh Court Battle Over Property Deal

Maradin, Dan Saran and Wakilin Watsa Labaran Zazzau Honour Loyal Aides with Traditional Titles