Majalisar Dattawa ta nemi a ɗauki matakin gaggawa kan tsaro a jihohin Arewa
Majalisar Dattawa ta nemi a ɗauki matakin gaggawa kan tsaro a jihohin Arewa
Majalisar dattawa ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakan gaggawa domin magance matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara, ciki har da yiwuwar dakatar da harkokin siyasa a wasu jihohin Arewa guda takwas da abin ya fi shafa.
Jihohin da aka ambata sun haɗa da Borno, Plateau, Bauchi, Benue, Niger, Sokoto, Kebbi da wasu sassan Kano, inda ake fama da hare-haren ‘yan ta’adda da rashin tsaro.
Wannan kira ya biyo bayan ƙorafin Sanata Abdul Ningi, wanda ya bayyana cewa matsalar tsaro na ƙaruwa, yana mai jaddada cewa lokaci ya yi da gwamnati za ta daina yin shiru tare da ɗaukar mataki mai ma’ana.
Majalisar ta kuma buƙaci a ƙara ƙaimi wajen ceto mutane 416 da ake zargin ƙungiyar Boko Haram ta sace a jihar Borno, waɗanda suka haɗa da mata, yara da tsofaffi.
Sanatocin sun nuna matuƙar damuwa kan yadda ake kai sabbin hare-hare kan sansanonin sojoji, suna mai cewa hakan na barazana ga tsaron ƙasa baki ɗaya. Sun kuma buƙaci hafsoshin tsaro da su sake duba matsalolin kayan aiki da dabarun yaƙi, tare da tabbatar da bin dokokin yaƙi da kare rayukan fararen hula.
Haka kuma, majalisar ta yaba wa sojojin rundunar Operation Hadin Kai bisa jajircewarsu wajen yaƙi da ‘yan ta’adda, tare da kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro bayanan sirri masu amfani.
Comments
Post a Comment