Mata sun jaddada goyon bayan su ga gwamnan Kaduna, Uba Sani da ya zarce zuwa wa'adi na biyu
Kungiyar mata a karamar hukumar Makarfi da ke jihar Kaduna sun gudanar da wani taro domin nuna goyon bayansu ga gwamnan jihar, Uba Sani da Shugaban Karamar Hukumar, Garba Muhammad Sabongari.
A yayin taron, shugabar mata ta shiyya ta daya a jihar, Hajiya Jummai Shuibu, ta bayyana cewa gwamnan da kuma shugaban karamar hukumar suna kokari wajen kawo ci gaba ga al’umma, musamman ga mata.
A wata sanarwa da Hadimin shugaban ƙaramar hukumar, Murtala Isah Qolo ya aikewa Daily Nigerian Hausa, Jimmai ta ce. "A wannan mulkin mu mata da yayanmu matasa, mun shaida kuma muka kwankwadi romon Demokaradiyya, domin Hon. Garba Sabon Gari Yana kulawa da mu, kuma yana Jin koken mu"
Ta kara da cewa za su ci gaba da zagayawa sassa daban-daban na yankin domin wayar da kan mata kan ayyukan alherin da shugaban karamar hukumar ke aiwatarwa a Makarfi, karkashin jagorancin Mai girma Gwamnan Jihar Kaduna.
Comments
Post a Comment