Obi ba zai iya dawowa ya tsaya takarar shugaban ƙasa ta 2027 a jam’iyyar mu ba – LP
Obi ba zai iya dawowa ya tsaya takarar shugaban ƙasa ta 2027 a jam’iyyar mu ba – LP
Shugabar riko ta jam’iyyar Labour Party (LP), Sanata Nenadi Usman, ta bayyana cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a 2023, Peter Obi, ba zai iya dawowa ya tsaya takarar 2027 a ƙarƙashin jam’iyyar ba.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa, Usman ta ce dokar zaɓe ta tanadi cewa dole ne jam’iyya ta rufe rajistar mambobinta kwanaki 21 kafin zaɓen fidda gwani, tare da miƙa sunayen ga Hukumar INEC, don haka ba zai yiwu a sake yi wa wani rajista bayan an rufe littafin ba.
Ta kuma amince cewa Obi ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasar LP a zaɓen 2023, inda har ya jawo mutane da dama, ciki har da ita kanta, suka bar PDP suka shiga jam’iyyar saboda adalci da daidaito.
Usman ta ce dalilin barinta PDP shi ne rashin bai wa yankin kudu tikitin shugaban ƙasa, abin da ta ce bai dace ba.
A halin yanzu, jam’iyyar LP na fama da rikicin shugabanci da ya janyo rabuwar kai da sauyin jam’iyya da dama. Kotu ta tabbatar da Usman a matsayin shugabar riko, duk da cewa tsohon shugaban jam’iyyar, Julius Abure, ya ce zai ƙalubalanci hukuncin a Kotun Koli.
Rikicin ya raunana jam’iyyar, inda ta rasa mambobi da ƙarfin tasiri, yayin da kuma aka ce Obi ya fice daga jam’iyyar ne sakamakon wannan rikici. Jam’iyyar ta kuma ware tikitin shugaban ƙasa na 2027 ga yankin kudu.
Comments
Post a Comment